Jadon Sancho: Man United ta kara farashin da ta fara taya dan wasan Dortmund

An wallafa

Manchester United ta kara farashin da ta fara taya dan kwallon Borussia Dortmund, Jadon Sancho zuwa fam miliyan 72.6.

Kungiyar Jamus ba ta sallama tayin farko da United ta yi wa matashin dan kwallon tawagar Ingila, mai shekara 21 ba.

Ana hasashen cewar Dortmund za ta amince da wannan tayin, watakila su karkare cinikin a kwanan nan, domin dan wasan ya je Old Trafford da wuri.

Kawo yanzu Sancho yana cikin tawagar kwallon kafa ta Ingila da ke buga gasar nahiyar Turai, wadda ta ja ragamar rukuni na hudu da maki bakwai.

Ingila ta kai zagayen gaba, tana kuma jiran wadda za ta hadu da ita a daf da na kusa da na karshe da wadda ta yi ta biyu tsakanin Faransa ko Jamus ko Portugal ko kuma Hungary.

Sanco ya koma Borussia Dortmund da taka leda daga Manchester City kan fam miliyan 10 a Agustan 2017.

Matashin dan wasan ya ci kwallo 50 a fafatawa 137 da ya yi wa Dortmund da kuma kwallo uku da ya ci wa Ingila a karawa 20 da ya yi mata.

A kaka uku da ya yi a Jamus yana da hannu a cin kwallo 109 a Dortmund.