Tottenham na daf da daukar Nuno Espirito Santo a matakin koci

Nuno Espirito

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Tottenham ta nada tsohon kocin Wolves, Nuno Espirito Santo a matsayin sabon kocinta kan yarjejeniyar kaka biyu.

Nuno ya bar aikin jan ragamar Wolverhampton a watan Mayu, bayan da ya kai kungiyar daga Championship zuwa Premier zuwa Europa League quarter finals.

Nuno ya maye gurbin Jose Mourinho wanda ta sallama cikin watan Afirilu.

Tun farko Tottenham ta tuntubi Mauricio Pochettino da kuma Antonio Conte, don maye gurbin dan kasar Portugal.

Kungiyar ta tuntubi Paolo Fonseca daga baya ta mayar da hankali wajen Gennaro Gattuso, wanda magoya baya suka yi zanga-zanga cewar ba sa bukatar a dauke shi kocin kungiyar.

An yi ta danganta wadanda za a bai wa kocin Tottenham tun farko ciki har da mai horar da Ajax, Erik ten Hag da na Leicester City, Brendan Rodgers.

Yanzu kuma abinda ya rage shi ne ko Harry Kane zai ci gaba da zama a kungiyar, bayan da yake son neman izinin Tottenham domin rashin lashe kofuna.

Tottenham za ta fara buga gasar Premier League cikin watan Agusta da Manchester City, amma za ta yi wasan sada zumunta da Leyton Orient ranar 17 ga watan Yuli.