Tokyo Olympic: Spain ba ta gayyaci Sergio Ramos ba

An wallafa

Tawagar kwallon kafa ta Sifaniya ta fitar da matasan 'yan wasa 22 da za su buga mata tamaula a gasar Olympic da birnin Tokyo zai karbi bakunci a bana.

Gasar dai ta matasa 'yan kasa da shekara 23 ce, amma an amincewa kowacce tawaga ta gayyaci manyan 'yan kwallo uku da suka haura shekarun ka'ida.

To sai dai Sifaniyar ba ta gayyaci Sergio Ramos a cikin manya uku don kare martabarta a fannin tamaula a gasar Olympic da za a fara a watan gobe ba.

Cikin wadanda ta gayyata sun hada da Dani Ceballos da Marco Asensio da kuma Mikel Merino.

Shi Ceballos yana da shekara 24, sauran biyun kuwa suna da 25, kuma karancin shekarun 'yan wasan da Sifaniya ta gayyata zuwa Olympic shi ne 21.

Ramos wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen watan Yuni a Real Madrid, ya sha fama da jinya a kakar da ta kare, wanda Sifaniya ba ta gayyace shi gasar kofin nahiyar Turai ba ta Euro 2020.

An tsayar da ranar 30 ga watan Yuni don 'yan wasan su taru wuri daya, wadanda koci Luis de la Fuente ya gayyata, koda yake shida daga ciki suna buga gasar nahiyar Turai da babbar tawagar Sifaniya.

'Yan wasan shida sun hada da Unai Simon da Eric Garcia da Pau Torres da Pedri da Mikel Oyarzabal da kuma Dani Olmo.

Bayan Ramos da ba a gayyata ba, da akwai wadanda aka yi mamakin rashin ba su goron gayyata da suka hada da Borja Mayoral da kuma Ferran Torres.

Sifaniya za ta buga wasan quarter finals da Switzerland ranar Juma'a, bayan da Sifaniya ta fitar da Croatia, ita kuwa Switzerland ta yi waje da Faransa ranar Litinin a Euro 2020.

'Yan wasan da Sifaniya ta gayyata wasan Olympic:

Masu tsaron raga: Alvaro Fernandez (Huesca) da Unai Simon (Athletic Club) da Alex Dominguez (Las Palmas).

Masu tsaron baya: Oscar Mingueza (Barcelona) da Jesus Vallejo (Granada) da Eric Garcia (Barcelona) da Pau Torres (Villarreal) da Oscar Gil (Espanyol) da kuma Juan Miranda (Real Betis).

Masu buga tsakiya: Marc Cucurella (Getafe) da Jon Moncayola (Osasuna) da Martin Zubimendi (Real Sociedad) da Dani Ceballos (Real Madrid) da Mikel Merino (Real Sociedad) da Carlos Soler (Valencia) da kuma Pedri (Barcelona).

Masu zura kwallaye a raga: Bryan Gil (Sevilla) da Marco Asensio (Real Madrid) da Dani Olmo (RB Leipzig) da Mikel Oyarzabal (Real Sociedad) da Rafa Mir (Wolves) da kuma Javi Puado (Espanyol).