Euro 2020: Shekarar 55 rabonda England ta cire Germany a sili daya kwale

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta kai wasan daf da na kusa da na karshe, bayan da ta doke Jamus da ci 2-0 a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai.
Ingila wadda ta taka rawa a kan Jamus a wasan da suka buga a zagaye na biyu a Wembley a gasar Turan ta ci kwallayen ta hannun Raheem Sterling da kuma Harry Kane.
Sterling, wanda shine ya ci Croatia da kuma Jamhuriyar Czech a wasan cikin rukuni, ya zura kwallo a ragar Jamus, bayan da ya samu kwallo daga bugun da Luke Shaw ya yi a minti na 75.
Harry Kane wanda karon farko kenan da ya tabuka abin a zo a gani ya ci kwallo na biyu ne a gaban 'yan kallo 40,000 a Wembley.
Golan Ingila, Jordan Pickford, wanda har yanzu kwallo bai shiga ragarsa ba, ya yi abin bajinta, bayan da ya hana kwallon da Timo Werner da kuma Kai Havertz suka buga masa shiga raga.
Tun farko Thomas Muller ya samu dama mai kyau da zai farke kwallon, amma ya buga ta yi fadi ta fita waje.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shine wasa na karshe da koci Joachim Low ya ja ragamar Jamus, wanda ya lashe kofin duniya da tawagar a 2014 a Brazil.
Tsohon mai horar da Bayern Munich, Hansi Flick - shine zai ci gaba da jan ragamar tawagar kwallon kafa ta Jamus.
Abubuwan tarihi da suka faru a wasan Ingila da Jamus:
Karon farko da Ingila ta caskara Jamus a Wembley a babbar gasa tun bayan kofin duniya a 1966, bayan da suka tashi wasa uku baya ba ci.
Tawagar Ingila ta zama ta biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai da ta yi wasa hudu kwallo bai shiga ragarta ba, bayan bajintar Jamus a 2016.
Rabonda Ingila ta yi wannan namijin kokarin tun kofin duniya da gasar cin kofin nahiyar Turai a 1966.
Sterling ya ci wa Ingila kwallo 15 a wasa 20 baya da ya buga a dukkan fafatawa, bayan 27 da ya yi bai ci kwallo ba a baya.
Kane ya ci tawagar Ingila kwallo 30 karkashin jagorancin Southgate, shine na biyu da ya ci kwallo da yawa karkashin koci daya, bayan Garry Lineker mai 35 karkashin koci Bobby Robson.
Kane ya yi kan-kan-kan da Wayne Rooney a cin kwallo bakwai a babbar gasa, bayan da Lineker ne kan gaba a Ingila mai 10, sai Alan Shearer mai tara a kofin duniya da gasar nahiyar Turai.
Muller ya buga wa Jamus dukkan wasa 26 a babbar gasa, kuma hakan ya sa ya yi kan-kan-kan da Mesut Ozil da ya fara bajintar tsakanin 2010 zuwa 2018.
Bukayo Saka mai shekara 19 da kwana 297 ya zama matashi mai karancin shekaru da ya yi wa babbar tawagar Ingila tamaula a sili daya kwale, bayan Wayne Rooney a Euro 2004 a quarter finals da Portugal yana da shekara 18 da kwana 244.











