Euro 2020: Spain ta kai wasan daf da na kusa da na karshe

Asalin hoton, Getty Images
Tawagar kwallon kafa ta Sifaniya ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai, bayan da ta doke Croatia ranar Litinin.
Sifaniya ta yi nasara ne da ci 5-3 a wasan da ya kayatar da suka fafata a Parken da ke Denmark karawar zagaye na biyu a gasar Turan.
Croatia ce ta fara cin kwallo, bayan da Sifaniya ta ci gida ta hannun Pedri minti 20 da fara tamauala, sai dai minti 18 tsakani Sifaniya ta farke ta hannun Pablo Sarabia.
Daga nan ta kara biyu ta hannun Cesar Azpilicueta da kuma wadda Ferran Torres ya zura a raga.
Saura minti biyar a tashi wasan ne Croatia ta zare kwalon ta hannun Mislav Orsic, sannan Mario Pasalic ya ci mata na uku daf da za a tashi, inda karawar ta koma 3-3.
Daga nan aka shiga karin lokaci, inda Sifaniya ta kara kwallo biyu ta hannun Alvaro Morata da wadda Mikel Oyarzabal ya ci.
Da wannan sakamakon Sifaniya za ta fafata a karawar quarter finals da duk wadda ta kai zagayen gaba tsakanin Faransa da Switzerland.






