'Euro 2020: Wadanda cutar korona ta hana su buga gasar Turai

An wallafa

An fara gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2020 ranar 11 ga watan Yuni a birane 11 da ke fadin nahiyar.

Sai dai kuma cutar korona ta ci gaba da kama wasu 'yan wasan da ke killace kansu, wasu ma har hakura suka yi da gasar.

Tuni dai wasannin na bana sun yi nisa, domin an kai fafatawar zagaye na biyu, har an fitar da mai rike da kofin Portugal da kuma Netherlands.

Tun a shekarar 2020 aka tsara gudanar da gasar cin kofin nahiyar Turai, amma bullar cutar korona ta sa aka dage wasannin zuwa bana.

'Yan wasan da suka kamu da cutar korana a Euro 2020:

CROATIA

* Ivan Perisic - ya kamu da cutar korona ranar 26 ga watan Yuni

Croatia ta kara da Sifaniya ba tare da Ivan Perisic ba a wasan zagaye na biyu, bayan da dan kwallon mai shekara 32 ya kamu da annobar.

INGILA

* Ben Chilwell - ya killace kansa ranar 21 ga watan Yuni

* Mason Mount - ya killace kansa ranar 21 ga watan Yuni

Ben Chilwell da kuma Mason Mount sun killace kansu har sai ranar 28 za su fito, ba su buga wa Ingila karawa da Jamhuriyar Czech ba, bayan da suka yi cudanya da dan wasan Scotland, Billy Gilmour, wanda ya kamu da cutar korona.

NETHERLANDS

* Jasper Cillessen - ya kamu da cutar korona ranar 28 ga watan Mayu

Mai tsaron ragar tawagar Netherlands ya hakura da gasar ta bana, bayan da ya kamu da annobar, kuma koci, Frank de Boer bai yi niyyar jiran sai ya warke ba.

PORTUGAL

* Joao Cancelo - ya kamu da cutar korona ranar 12 ga watan Yuni

Mai tsaron bayan tawagar Portugal bai samu shiga wasannin bana ba, bayan da ya kamu da annobar, inda Diogo Dalot ya maye gurbinsa, bai samu buga wasan da tawagar ta yi da Hungary ba.

RASHA

* Andrei Mostovoy - ya kamu da cutar korona ranar 11 ga watan Yuni

Rasha ta maye gurbin Andrei Mostovoy da mai tsaron baya Roman Yevgenyev, sakamakon da Mostovoy ya kamu da annobar.

SLOVAKIA

* Denis Vavro - ya kamu da cutar korona ranar 17 ga watan Yuni

Mai tsaron baya Denis Vavro da wani mamba a tawagar sun kamu da annobar a karawar da za suyi da Sweden.

Sai dai koci, Stefan Tarkovic ya ce dukkansu suna cikin koshin lafiya, ba alamar kamuwa da annobar a jikinsu.

Sifaniya

* Sergio Busquets - ya kamu da cutar korona ranar 6 ga watan Yuni

kyaftin Sergio Busquets ya kamu da annobar kwana takwas kan wasan farko da Sifaniya za ta kara da Sweden, saboda haka bai buga karawar ba.

Shi kuwa mai tsaron baya, Diego Llorente ya kamu da cutar kwana biyar kan Sifaniya ta yi karawar farko ta cikin rukuni da Sweden.

SWEDEN

* Dejan Kulusevski - ya kamu da cutar korona ranar 8 ga watan Yuni

* Mattias Svanberg - ya kamu da cutar korona ranar 8 ga watan Yuni

Dan wasa Dejan Kulusevski da kuma Mattias Svanberg ba su buga wa Sweden wasan farko na cikin rukuni da Sifaniya ba, sakamakon kamuwa da cutar korona.

Bayan da tawagar ta buga wasan farko ne 'yan wasan biyu suka koma yi mata tamaula, bayan da aka kara gwada su ba a samu cutar a jikinsu ba.