Euro 2020: Abinda ya kamata ku sani kan wasan Belgium da Portugal

Lukaku Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Belgium da Portugal za su kara a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin nahiyar Turai ranar Lahadi a Estadio Olimpico de la Cartuja da ke Spaniya.

Belgium ita ce ta daya a jerin wadanda ke kan gaba a kwallon kafa a duniya, ita kuwa Portugal ita ce mai rike da kofin nahiyar Turai.

Wannan shi ne karon farko da za su kece raini a tsakaninsu a wata babbar gasar tamauala.

Portugal ba ta yi rashin nasara a kara uku baya da ta yi da Belgium ba, tun bayan doke ta 3-2 a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya a Satumbar 1989.

Kenan Portugal ta yi nasara a karawa uku da canjaras biyu kenan, kuma duk wadda ta yi nasara za ta kai fafatawar Quarter finals kenan.

Tawagar Belgium:

Wasa biyu ne kacal Belgium ba ta ci ba daga 58 da ta buga karkashin Roberto Maryinez.

Kevin de Bruyne yana da hannu a cin kwallo uku daga bakwai da tawagar ta zura a raga gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana, wanda ya ci daya ya bayar da biyu aka zura a raga.

Nasarar da Belgium ta yi a kan Finland ita ce ta tara da Roberto Martinez ya ci a kofin duniya da gasar nahiyar Turai, hakan ya sa ya zama kan gaba a mai horar da kasar da ke kan gaba a nasara.

Tawagar Portugal:

Kawo yanzu an zura kwallo shida a ragar Portugal a wasa uku a rukunii a gasar bana, bayan da a Euro 2016 kwallo biyar aka zura mata, kuma ita ce ta lashe kofin.

Portugal ta kai zagaye na biyu a mataki na uku a rukuni na shida, kuma karo na biyu, bayan da ta yi hakan a 2016 da ya kai ta zama zakara a karon farko a Turai.

Maki hudu daga wasa ukun da Portugal ta hada a rukuni na shida, shi ne rashin kokari da mai rike da kofi ta yi a karon farko tun bayan wanda Girka ta yi a 2008.