Euro 2020: Rukunin kare jini biri Faransa, Jamus da Portugal

Asalin hoton, Getty Images
Ingila ta shiga rukuni daya da kasashen Croatia da jamhuriyar Czech a gasar EURO 2020, inda Wales tare da Italy, Switzerland da Turkiyya ke rukunin farko.
Jamus za ta fafata da mai rike da kofin duniya wato Faransa da kuma me dauke da kofin gasar ta turai wato Portugal a rukunin F.
Wadanda suka yi nasara a wasan cike gurbi na Scotland, da suka kunshi kasashen Norway, Serbia da Isra'ila, za su kara da Ingila a rukunin D.
Ingila wadda ta je zagayen dab da na karshe a gasar cin kofin duniya za ta fara wasanta na farko da Croatia a Wembley ranar 14 ga watan Yuni.
Wasan farko na bude gasar Italiya ce za ta karbi bakuncin Turkiyya a Rome ranar 12 ga watan Yuni.
Scotland, Ireland ta Arewa da jamhuriyar Ireland dukkaninsu za su fito a wasan cike gurbi a watan Maris mai zuwa, inda kungiyoyi 16 zasu fafata domin cike gurbin hudun karshe.
Gasar wadda za ta gudana a birane 12 da ke kasashen Turai , kasashen nahiyar daban-daban ne zasu karbi bakunci a karon farko don murnar bikin cika shekaru 60 da fara yin ta.
Jadawalin gasar da aka fitar
- Rukunin A: Italiya, Switzerland, Turkiyya, Wales
- Rukunin B: Belgium, Rasha, Denmark, Finland
- Rukunin C: Ukraine, Netherlands, Austria
- Rukunin D: Ingila, Croatia, Jamhuriyar Czech
- Rukunin E: Sifaniya, Poland, Sweden
- Rukunin F: Jamus, Faransa, Portugal
Idan Ingila ta samu nasara a rukuninsu, wasanta na dab da na kusa da na karshe zata yi shi ne a Dublin, kuma zata fafata ne da daya daga cikin kasashen da ke rukunin F, wanda ya kunshi kasashen Jamus, Faransa da kuma Portugal.
Wannan ne karo na biyu da aka sanya kasasahen da suka lashe gasar cin kofin duniya da kuma kasar da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai a rukuni guda, tun bayan gasar Euro da aka yi a shekarar 1992, lokacin da kasar Netherlands ta doke Jamus.
Jamus wadda ta lashe gasar cin kofin duniya a 2014, za ta karbi bakuncin wasanni uku da za ta yi a birnin Munich, sai kuma wasa daya a Budapest. Idan har Hungary ta ci wasanta na cike gurbi zata kasance a rukunin F, inda zata karbi bakuncin wasanni biyu.
"Wannan rukuni ne na kare jini biri jini," inji kocin Jamus boss Joachim Low.
Shin Ingila zai fi mata dama-dama ne ta fito ta biyu a rukuninsu?
A wani yanayi mai kama da wannan ga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2018, da alama Ingila za ta iya karewa ta biyu a rukuninsu.
Wadanda suka yi nasara a rukunin da Ingila ke ciki za su kara ne da daya daga cikin kasashen da ke rukuni na shida - da alama dai Jamus, Faransa ko Portugal - a Dublin.
Amma idan Ingila ta fito a rukunin a matsayin ta biyu to za ta yi wasanta ne da daya daga cikin kasashen da ke rukuni na biyar wato Spain, Poland Sweden ko kuma Ireland ta Arewa ko Jamhuriyar Copenhagen.
Bugu da kari, kasashen da za su tsallaka zagayen gab da na kusa da karshe za su iya kasancewa masu tsanani - watakila Spain a St Petersburg idan ta yi nasara a rukuninsu.










