Ana tattaunawa yadda za a daga gasar Euro 2020

Uefa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bayan gasar maza ta mata ma ana shirin daga ta zuwa nan gaba
An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Turai Uefa ta kira taron gaggawa domin duba yuwuwar daga gasar Euro 2020 zuwa nan da shekara daya.

Hukumar Uefa za ta yi taron manema labarai domin bayyana matakan da ake dauka kan wannan annobar ta Coronavirus.

Tattaunawar za ta hada da wasannin cikin gida na LIg da kuma gasannin nahiyar Turai ciki har da Euro 2020.

An tsara gudanar da gasar Euro 2020 ne daga 12 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yuli a filaye daban daban a fadin Turai.

Uefa ta gayyaci wakilan kungiyoyi daban-daban har 55, ciki har da wakilan kungiyar kuloblika na kasashe.

Ita kuma gasar mata ta Euro an tsara gudanar da ita ne a Ingila daga 11 ga watan Yuli zuwa daya ga watan Agusta 2021.