Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Nuno da Pellegrini da Haaland da Niguez da Silva da Loftus-Cheek, Neves da Willems

An wallafa

Tsohon kocin Wolves Nuno Espirito Santo na gab da daidaitawa da Crystal Palace a matsayin sabon kocinta. (Telegraph, subscription required)

Atletico Madrid ta miƙa tayinta ga ɗan wasan tsakiyarManchester City Saul Niguez, mai shekara 26, da neman musaya da ɗan wasan gaba Bernardo Silva, shi ma ɗan shekara 26. (Times)

Liverpool ta aike tayin £25.8m kan kyeftin ɗin Roma, asalin Italiya Lorenzo Pellegrini, mai shekara 24, domin maye gurbin Georginio Wijnaldum. (Corriere dello Sport, via Sun)

Arsenal ta sanar da tayin £20m kan ɗan wasan Sifaniya Hector Bellerin, yayin da ita ma Atletico Madrid ta nuna kwaɗayinta domin maye gurbin ɗan wasan Ingila Kieran Trippier, wanda ake tunanin zai komaManchester United. Real Betis ita ma ta nuna zawarcinta a kan Bellerin, sai dai cinikin zai kasance kan tayin da ta gabatar. (CBS Sport)

Ana zargin Juventus na son ɗauke Bellerin da yiwuwar musaya da ɗan wasan Wales Aaron Ramsey. (Sport, in Spanish)

Ɗan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, ya zaƙu ya koma taka leda a Chelsea kuma a shirya yake ya yi zaman jiran shekara guda. (Telegraph, subscription required)

Mai bugawaLiverpool da Japan gaba Takumi Minamino, ana tunanin zai koma Southampton inda ya yi zaman aro a kakar da ta gabata. (HampshireLive)

Kocin Brighton Graham Potter na nazarin karɓar aikin horar da Everton bayan tafiyar Carlo Ancelotti. (Athletic, subscription required)

Arsenal ta shiga tattaunawa da Wolves kan ɗan wasan tsakiya Ruben Neves, yayin da ƙungiyar ta zaku ta maye gurbin Xhaka, ɗan shekara 28, wanda ke gab da koma wa Roma. (Goal)

Bayern Munich ta sake bayyana sha'awarta kan ɗan wasan ChelseaCallum Hudson-Odoi, mai shekaru 20. (Times, subscription required)

Ɗan wasanArsenal mai shekara 23 Ainsley Maitland-Niles, na son samun tabbaci kan makomarsa daga kocinsu Mikel Arteta. (Telegraph)

A gefe guda kuma kocin Roma Jose Mourinho ya nuna zawarcinsa kan mai tarar ragar Wolves Rui Patricio, ɗan shekara 33. (Sky Italia - in Italian)

Dan wasan tsakiyar Sifaniya Dani Ceballos, ya shaida cewa yana son komawa domin buga La Liga a kaka mai zuwa bayan kammala zaman aro a Arsenal daga Real Madrid. (Cadena SER, via Evening Standard)

Roy Hodgson ya yi watsi da tayin West Brom na zama sabon kocinta. (Football Insider)

Ɗan wasan Dutch Jetro Willems, mai shekara 27, na son koma wa Newcastle bayan baro Eintracht Frankfurt. (Chronicle)

Matashi ɗan wasan Chelsea da Ingila Ruben Loftus-Cheek, na cikin ƴan wasan da tsohon kocin Chelsea Maurizio ke son farauta da zarar ya koma Lazio. (Corriere dello Sport - in Italian)

AC Milan na tattaunawa da Chelsea kan sayen ƴan wasanta uku, Olivier Giroud da Hakim Ziyech da Fikayo Tomori. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Ana sanar da AC Milan cewa sayen ɗan wasan Sifaniya Brahim Diaz kan yarjejeniyar dindindin daga Real Madrid za ta kai £26m, sai dai kungiyar ta La Liga na neman dauko ɗan aro. (Goal)