Karim Benzema: Watakila dan wasan ya yi rauni a gwiwar kafa

An wallafa

Tawagar kwallon kafa ta Faransa ta caskara ta Bulgaria da ci 3-0 a wasan sada zumunta da suka kara ranar Talata.

Faransa ta buga wasan sada zumuntar ne domin shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin nahiyar Turai da za a fara ranar Juma'a.

Sai dai kuma a karawar an sauya dan wasan Real Madrid, Karim Benzema tun kan hutu, bayan raunin da ya yi da wasu ke hasashen a gwiwar kafarsa ne.

An sauya dan wasan ne saura minti hudu kungiyoyin su je hutu, bayan da ya yi tsalle ya sakawa kwallo kai sai ya fado a kan kafarsa ba kamar yadda ya kamata ba.

A makon jiya Faransa ta gayyaci Benzema cikin tawagar, tun bayan shekara biyar rabon da ya buga mata tamaula.

Benzema ya zauna a kan benci bayan da aka sauya shi, inda likitoci suka duba raunin da ya yi.

Faransa za ta fara wasan cikin rukuni da Jamus ranar Talata 15 ga watan Yuni.