Wasu 'yan wasan Turai da ba za su buga Euro 2020 ba

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Juma'a za a fara gasar cin kofin nahiyar Turai da kasashe 24 za su barje gumi a tsakaninsu a bana.
Tun a bara ya kamata a gudanar da gasar da Portugal ke rike da kofin, amma cutar korona ta kai tsaikon da aka dage karawar zuwa bana.
Sai dai kuma kawo yanzu akwai fitattun'yan wasa biyar da suka taka rawar gani a kwallon nahiyar Turai, amma ba za su buga gasar da za a fara ranar Juma'a ba.
Cikinsu har da dan kwallon tawagar Norway da Borussia Dortmund, Erling Haaland wanda kasarsa ba ta samu tikitin shiga wasannin ba.
Sauran sun hada da dan wasan tawagar Sweden, Zlatan Ibrahimovic da Sergio Ramos na Sifaniya da na tawagar Netherlands Virgil van Dijk.

Asalin hoton, Getty Images
Erling Haaland, dan kwallon tawagar Norway mai shekara 20:
Kamar yadda ake fada dan kwallon ya kai darajar Yuro miliyan 100 a kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo, kuma Haaland shi ne fitaccen dan wasa da ke kan ganiya da ba zai buga gasar nahiyar Turai ba.
Haaland ya yi wa Norway wasa biyu na neman shiga gasar Turan da na cike gurbi guda daya, kuma bai ci kwallo ba da kasar ta kasa kai banten ta a karon farko tun 2000.

Asalin hoton, Getty Images
Zlatan Ibrahimovic, dan wasan tawagar Sweden mai shekara 39.
Kowa ya yi mamaki da aka ji sanarwar cewar dan kwallon AC Milan zai koma buga wa Sweden tamaula, bayan shekara biyar da yin ritaya.
Wani kwallo da ya ci Italiya a gasar 2004 daya ne daga mafi kayatarwa da aka zura a raga a tarihin gasar nahiyar Turai.
Ibrahimovic ya bayar da kwallo biyu aka zura a raga a wasa biyu da ya yi wa tawagar a karawar neman gurbin shiga gasar bana, sai dai kuma raunin da ya yi a gwiwar kafa ya hana shi zuwa buga wasannin bana.

Asalin hoton, Getty Images
Sergio Ramos, dan wasan tawagar Sifaniya, mai shekara 35:
Da dan kwallon Real Madrid da Sifaniya ya buga gasar cin kofin nahiyar Turai ta bana da ya zama kan gaba a yawan buga wasanni mai 180.
Sai dai kuma kocin na Sifaniya bai zabi gayyatar kyaftin Ramos ba, wanda ya lashe gasar Turai a 2008 da kuma a 2012, sakamakon raunin da yake ta jinya.

Asalin hoton, Getty Images
Ansu Fati, dan kwallon tawagar Sifaniya, mai shekara 18:
Ana kwatanta dan wasan Barcelona da cewar yana da kwarewar murza leda da zura kwallaye a raga kamar yadda ya yi a Lik da kuma a Champions League.
Ya kafa tarihin matashin da ya ci wa Sifaniya kwallo, sai dai kuma ba zai samu damar buga wa kasar babbar gasar ba, sakamakon raunin da ya yi a Nuwamba, kuma har yanzu bai warke ba.

Asalin hoton, Getty Images
Virgil van Dijk, dan wasam Netherlands, mai shekara 29:
Dan wasan Netherlands shi ne ake alakantawa da mai tsaron baya mafi fice kawo yanzu, mai taka leda a Liverpool.
Sai dai kuma dan wasan ya ci karo da koma baya, sakamakon raunin da ya yi da hakan ya kai tsaiko ga wasannin Liverpool, kuma dan kwallon bai warke ba da hakan ya kasa yi wa kasar wasan farko











