Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Pirlo, Grealish, Ziyech, Tomori, Alli, Buendia

An wallafa

Andrea Pirlo da tsohon kocin Chelsea Maurizio Sarri na cikin kociyan da ke kan gaba wajen samun aikin horas da Everton kuma Pirlo ma ya fara tattaunawa da mai kungiyar Farhad Moshiri. (Calciomercato via Liverpool Echo)

Jack Grealish, dan wasan tsakiya na Aston Villa da kuma Ingila mai shekara 25 na iya ci gaba da zamansa a kungiyar a kakar wasa mai zuwa saboda Manchester City da Manchester United sun gaza biyan fam miliyan 130 da aka dora kan dan wasan. (Talksport)

Dan wasan tsakiya na Manchester City da Brazil, Fernandinho, mai shekara 36 da Andy Carroll mai shekara 32 na Newcastle na cikin 'yan wasan da kungiyoyinsu su ka tabbatar za su ci gaba da zamansu a kakar wasa mi zuwa. (Premier League)

Manchester City na daf da sauko Metinho, dan wasan tsakiya na Fluminense mai shekara 18, kuma wanda aka fi sani da sunan "Paul Pogban Brzil". (Goal)

Chelsea ba ta cire ran sayar da Hakim Ziyech, dan wasan gefe mai shekara 28 ga AC Milan ko Napoli ba. (Calciomercato - in Italian)

AC Milan ta sanar da Chelsea cewa za ta bukaci a biya ta fam miliyan 28.5 kafin ta iya sayen Fikayo Tomori dan wasan baya mai shekara 23. (Fabrizio Romano)

'Yan wasan Everton sun "gigice matuka" bayan da ta tabbata Carlo Ancelotti zai koma Real Madrid, inda Richarlison mai shekara 24 dan Brazil, da James Rodriguez, dan Colombia mai shekara 29 su ka fara tunanin barin kungiyar . (The Athletic - subscription required)