Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sergio Aguero ya koma Barcelona daga Manchester City
Dan wasan Argentina Sergio Aguero ya koma Barcelona da taka leda.
Ɗan wasan ya ƙulla yarjejeniyar shekara biyu da Barcelona kuma zai koma ƙungiyar ne idan ƙwangilarsa ta ƙare a Manchester City a ƙarshen watan Yuni.
Barcelona ta tabbatar da ɗauko ɗan wasan a shafinta na Twitter inda ta rubuta sunansa tare da wallafa hotonsa sanye da rigar ƙungiyar.
Ɗan wasan na Argentina, mai shekara 32, ya bar City ne bayan shafe shekara 10 a kulub ɗin na Manchester, inda ya zama ɗan wasan da ya fi kowa cin kwallaye a tarihi.
Sergio Aguero ya ci kwallaye 260 a wasa 390 da ya buga wa City.
Ya buga wa City wasan ƙarshe a fafatawar da ta sha kashi hannun Chelsea wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai a ranar Asabar.
Yanzu duk ƙungiyar da ke son sayen Aguero sai ta ajiye wa Barcelona fam miliyan 86.
Ɗan wasan zai hadu da tsohon abokin wasansa Lionel Messi wanda suka fara taka leda tun kuriciya a Argetina