'Yan Real Madrid da suka tashi 2-2 da Sevilla a La Liga

La Liga

Asalin hoton, Real Madrid

An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Sevilla a wasan mako na 35 da za su fafata ranar Lahadi a Alfredo Di Stefano.

Kungiyoyin sun hadu ranar 5 ga watan Disamba a wasan farko a La Ligar bana, inda Real ta yi nasara da ci 1-0, bayan da mai tsaron gidan Sevilla, Bono ya ci gida.

Real Madrid tana mataki na uku a kan teburin La Liga da maki 74 da tazarar maki daya tsakaninta da Barcelona ta biyu mai maki 75.

Ita kuwa Sevilla mai fatan samun gurbin shiga Champions League a badi tana mataki na hudu a teburin Spaniya da tazarar maki hudu tsakaninta da Real Madrid ta uku.

Ranar Asabar Barcelona da Atletico Madrid suka tashi 0-0 a Camp Nou, hakan ya sa Atletico ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi da maki 77.

To sai dai idan Real Madrid ta ci Sevilla a ranar ta Lahadi za ta dare kan teburin gasar bana kenan, bayan da ta ci Atletico a haduwa da suka yi a La Ligar nan.

A cikin watan Disamba suka fara fafatawa a gasar Spaniya ta bana, inda Real ta ci 2-0 a gida, sannan suka tashi 1-1 a gidan Atletico cikin watan Maris a wasa na biyu.

Tuni kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasan da za su fuskanci Sevilla a karawar mako na 35 a gasar ta La Liga ranar Lahadi.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya: E. Militao da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma Miguel.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Isco da kuma Blanco.

Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Mariano and Rodrygo.

Yadda 'yan biyar din teburin La Liga yake da yawan wasa da yawan maki:

  • Atletico Madrid35 77
  • FC Barcelona35 75
  • Real Madrid CF34 74
  • Sevilla FC34 70
  • Real Sociedad35 56