Abin da ya kamata ku sani kan wasan Man City da PSG

An wallafa

Paris St Germain ta ziyarci Manchester City, domin buga wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su kara a Etihad ranar Talata.

A makon jiya ranar Laraba ne City ta yi nasara a kan PSG da ci 2-1 a Faransa.

Wannan shi ne wasa na biyar da za su fafata a gasar Zakarun Turai, inda City ta yi nasara a karawa biyu da canjaras biyu.

Karon farko kenan da Guardiola ya kai wasan daf da karshe a Champions League tun bayan da ya koma horar da tamaula a Etihad a 2016.

Zai kuma fuskanci kalubale a wajen PSG wadda ta kai wasan karshe a bara, wadda ta fitar da Barcelona da kuma Bayern Munich mai rike da kofi a bana.

Tuni dai Paris St Germain ta bayyana 'yan wasan da za su fuskanci Manchester City a Etihad a wasa na biyu da za su fafata.

Mbappe dan kwallon tawagar Faransa ya ci kwallo 37 a wasa 43 a dukkan fafatawa a bana, har da guda goma a Champions League a kakar nana.

Manchester City ta yi rashin nasara a wasa biyu daga biyar baya da ta fafata bayan nan a dukkan karawa da ta yi, wato jumulla cikin wasa 33 ta yi rashin nasara a uku.

Pochettino da Guardiola sun fuskanci juna sau 19, inda kocin PSG ya yi nasara sau uku, shi kuwa na City ya lashe 11 da canjaras biyar.

Wasan karshe da aka ci City a waje shi ne wanda Shakhtar Donetsk ta yi nasara da ci 2-1 a Champions League a kakar 2017/18.