2021 Afcon qualifier: Super Eagles za ta kara da Lesotho a Legas

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF za ta karbi bakuncin Lesotho a jihar Legas a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Hukumar ta ce tawagar ta Najeria za ta buga wasan ne a Teslim Balogun ranar Talata 30 ga watan Maris, kamar yadda ta sanar a shafinta na sada zumunta.

Kwana uku kafin fafatawa da Lesotho, Super Eagles za ta ziyarci Benin a karawar da za su yi a filin wasa na Charles De Gaulle da ke Porto Novo.

Har yanzu Super Eagles ba ta yi rashin nasara a wasa hudu da ta buga a cikin rukuni ba, bayan da ta ci biyu da canjaras biyu, ita ce kan gaba a rukunin na 12.

Najeriya tana da maki takwas, sai Benin ta biyu da maki bakwai, Saliyo mai maki uku tana ta uku, sannan Lesotho ta karshe mai maki biyu.

Rabonda tawagar Najeriya ta taka leda tun cikin watan Nuwamba, bayan da ta tashi ba ci da Benin a Najeriya.

Wannan ita ce gasa ra 19 da Super Eagles ke fatan halartar wasannin cin kofin nahiyar Afirka, tun bayan da ta fara buga gasar a 1963 da Ghana ta karbi bakunci.

Kasar Kamaru ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka, kuma karo na 33 da nahiyar ke gudanar da wasannin.

Tun farko ranar 9 ga watan Janairun 2021 ya kamata Kamaru ta karbi bakuncin gasar daga baya aka mayar zuwa Janairun 2022.

Algeria ce mai rike da kofi da ta lashe gasar da aka yi a Masar a 2019, bayan da ta doke Senegal da ci 1-0 a wasan karshe.