Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Buhari ya jinjina wa Super Eagles
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Super Eagles murnar nasarar doke Iceland a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Tawagar Super Eagles ta doke Iceland ne 2-0 a wasa na biyu a rukunin D da suka fafata a ranar Juma'a.
Ahmed Musa ne ya ci wa Najeriya dukkanin kwallayen biyu a ragar Iceland, wanda ya ba shi damar zama dan wasan Najeriya da ya fi yawan cin kwallaye a gasar cin kofin duniya.
Shugaba Buhari ya bayyana farin ciki tare da jinjina wa 'yan wasan na Najeriya musamman yadda suka nuna kwazo a wasan.
Ya bukaci 'yan wasan kada su yi kasa a guiwa, inda ya bukaci su doke Argentina kamar yadda suka lallasa Iceland.
"Na tabbatar da cewa idan 'yan wasanmu sun yi imani da kansu za su iya tsallakewa daga rukuninsu mai wahala har ma su kara samun ci gaba a gasar." a cewar shugaban na Najeriya.
Wasan Najeriya da Iceland ya ja hankalin 'yan Najeriya bayan Croatia ta doke Argentina 3-0.
Mataimakin shugaban Najeriya ya kalli wasan Najeriya da Iceland ne yayin da yake cikin mota a kan hanya a Lagos.
Shugaban Majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki ya tafi har Rasha domin mara wa Super Eagles baya.
An nuna hoton dan siyasar na Najeriya yana murna a cikin 'yan kallo.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ma ya kalli wasan.
A wasan farko, Najeriya ta sha kashi ne 2-0 a hannun Croatia.
A ranar 26 ga wata Najeriya za ta fafata a Argentina, wasan da zai tantance makomar kasashen biyu.
Najeriya za ta kai zagaye na gaba idan ta doke Argentina.
Haka ma Najeriya za ta iya tsallakewa idan ta yi canjaras da Argentina amma sai idan Croatia ta doke Iceland ko kuma suka yi canjaras.