Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Coman, Ceballos, Cavani, Mbappe, Messi, Torres, Lacazette
Bayern Munich tana fargabar cewa Manchester Unitedza ta kwace mata dan wasanFaransa Kingsley Coman, mai shekara 24, saboda alawus-alawus din da ke cikin kwangilar da za ta ba shi. (Bild, via Mail)
Arsenal na son daukar dan wasan SifaniyaDani Ceballos, mai shekara 24, da golan Australia Mat Ryan, mai shekara 28, a matakin dindindin a bazarar nan. 'Yan wasan biyu suna zaman aro a Gunners daga Real Madrid da Brighton. (Sun)
Dan wasanManchester United da Uruguay Edinson Cavani yana son zama a Old Trafford zuwa karin kakar wasa daya. A bazarar da ta wuce ne dan wasan mai shekara 34 ya kulla yarjejeniyar shekara daya da kungiyar. (Telegraph - subscription required)
Paris St-Germain ta sanya farashin euro 200m (£173m) kan dan wasan Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, wanda Real Madrid, Liverpool, Manchester City da kuma Juventussuke son saya. (La Parisien - in French)
Mbappe ya ce yana cike da farin cikin zama a PSG kuma zai yanke hukunci game da makomarsa ne ta hanyar yin zurfin tunani, bayan nasarar da suka yi da ci 4-1 a kan Barcelonaranar Talata. (FourFourTwo)
Barcelona ta so daukar Mbappe a 2017 amma ta zabi sayen dan wasan Faransa mai shekara 22 Ousmane Dembele daga Borussia Dortmund. (Mirror)
Dan takarar shugabancin Barcelona Joan Laporta ya yi alkawarin yin "dukkan mai yiwuwa" domin rarrashin dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, ya ci gaba da zama a kungiyar. (Sky Sports)
Real Madrid na duba yiwuwar daukar dan wasanVillarreal dan kasar Sifaniya Pau Torres, mai shekara 24. (Goal)
Thierry Henry da tsohon abokin tamaularsa a Arsenal Patrick Vieira suna gogayya wajen neman mukamin mai horas da 'yan kwallo a Bournemouth. (Talksport)
Dan wasan Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 29, yana cikin 'yan wasa da dama da Arsenal za ta iya sayarwa a bazarar domin rage kashe kudi. (Sun)
Dan wasa Brazil David Luiz, mai shekara 33, dan wasan Uruguay Lucas Torreira, mai shekara 25 da kuma dan wasan Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 21, suna son barin Arsenal. (Star)
Dan wasanAtletico Madrid da Uruguay Luis Suarez, mai shekara 34, ya ce zai yanke shawara kan lokacin da zai yi ritaya daga tamaula, amma ya kara da cewa zai kwashe karin shekaru yana murza leda. (ESPN)
Babu tabbacin cewa dan wasan Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, zai samu damar tafiya Barcelona idan ya bar Liverpool a bazara, saboda matsalar rashin kudin da Barca ke fama da ita. (Liverpool Echo)