Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Messi, Haaland, Sancho, Upamecano, Alli, Raphinha da Saliba

Lionel Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin Paris St-Germain Mauricio Pochettino ya dage cewa kungiyarsa da kuma 'yan wasanta ba su nuna "rashin da'a ba" saboda kawai sun bayyana sha'awarsu ta daukar dan wasan Barcelona dan kasar Argentina Lionel Messi, mai shekara 33. (ESPN)

Manchester City za ta dauki sabon dan wasan gaba a bazara ko sun yi nasarar sayen Messi ko ba su yi ba, inda suka mayar da hankali wajen daukar dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20. (90 Min)

Kazalika Dortmund na duba yiwuwar sayar da 'yan wasa bakwai a bazarar nan, ciki har da dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (Mirror)

Dan wasan Belgium Axel Witsel, mai shekara 32 da dan wasan Amurka Giovanni Reyna, mai shekara 18, da dan wasan Ingila Jude Bellingham, mai shekara 17, da kuma Haaland na cikin 'yan wasan da za a iya sayarwa, inda Dortmund ta matsu ta tara kudi. (Waz, via Express)

Kocin Chelsea Thomas Tuchel ya ki ya tsoma cikin jita-jitar da ake yi game da yiwuwar ya dauki Haaland da kuma dan wasan RB Leipzig dan kasar Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 22. (ESPN)

Tuchel yana so dan wasan PSG dan kasar Faransa Kays Ruiz-Atil, mai shekara 18, ya bi shi zuwa Stamford Bridge. (Foot Mercato, via Team Talk)

Jose Mourinho ya amince cewa watakila hankalin dan wasan Ingila Dele Alli, mai shekara 24, ya rabu biyu saboda rade radin da ake yi cewa zai tafi Tottenham a watan jiya. (London Evening Standard)

Liverpool tana son daukar dan wasan Leeds United dan kasar Brazil Raphinha, mai shekara 24, a bazara. (France Football, via Mail)

Udinese ba ta kawar da yiwuwar sayar da dan wasan Argentina Rodrigo de Paul, mai shekara 26 ba a bazara bayan rade radin da suka alakanta si da son tafiya Liverpool a watan Janairu lokacin cinikin 'yan kwallo. (Goal)

West Brom ta yanke shawarar kin bai wa Ahmed Musa kwangila bayan dan wasan na Najeriya mai shekara 28 ya murza leda ta dan wani lokaci a kungiyar. (Express & Star)

Mataimakin manajan Aston Villa John Terry yana cikin jerin mutum biyar da suke iya zama kocin Bournemouth. (Birmingham Mail)