Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Shawcross, Gibbs, Martinez, Solskjaer, Ibrahimovic, Stones, Ederson da Hodgson

Asalin hoton, Getty Images
Inter Miami, kungiyar kwallon kafa ta Major League wadda David Beckham ya kafa kuma Phil Neville ya yi mata manaja, tana son daukar tsoffin 'yan wasan Ingila biyu - Ryan Shawcross, mai shekara 33, daga Stoke City da kuma Kieran Gibbs, mai shekara 31, daga West Brom. (Sun)
Manchester City za ta daina zawarcin dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, a yayin da ake sa ran dan wasan mai shekara 23 zai sabunta kwangilarsa a Milan. (Eurosport)
Manchester United za ta jira zuwa karshen kakar wasa kafin ta soma tattaunawa kan kwangilar dan kasar Norway Ole Gunnar Solskjaer, wanda kwangilarsa ta yanzu za ta kare a karshen kakar wasa ta 2021-22. (Sun)
Real Madrid ta samu tagomashi a yunkurin daukar dan wasan Bayern Munich da Austria David Alaba, mai shekara 28, a yayin da Chelsea ta ce ba za ta iya biyan alawus-alawus dinsa na mako-mako wanda ya kai £400,000 ba. (ESPN)
AC Milan na shirin soma tattaunawa da dan wasan Sweden Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 39, kan sabunta kwangilarsa abin da zai sa ya ci gaba da zama a kungiyar nan da shekara biyu. (Sun)
Manchester City za ta soma tattaunawa kan kwangilar John Stones, mai shekara 26, a bazarar nan domin nuna jin dadi game da rawar da dan wasan yake takawa a kokarin kungiyar na daukar kofi. (Times, subscription required)
Crystal Palace ba ta da tabbacin sabunta kwangilar kocinta Roy Hodgson, mai shekara 73, a kakar wasa mai zuwa. Kwangilar tsohon kocin na Ingila za ta kare a bazara. (Mail)
Dan wasan Newcastle United dan kasar Ingila Dwight Gayle, mai shekara 31, ba ya jin dadin rashin sanya shi a wasa akai-akai a St James' Park kuma zai iya barin kungiyar idan kwangilarsa ta kare a bazara. (Chronicle)
Golan Sweden Robin Olsen, mai shekara 31, yana son ya mayar da zaman aron da yake yi a Everton daga Roma na dindindin. (Goal)
Kocin Manchester City Pep Guardiola yana duba yiwuwar barin golan Brazil Ederson, mai shekara 27, ya rika yin bugun fenareti - a yayin da kungiyar ta zubar da uku cikin bakwai na bugun fenaretin da ta samu. (Independent)











