Ronaldo ya bai wa Lukaku tazarar kwallo biyu a Serie A

An wallafa

Juventus ta doke Roma da ci 2-0 a wasan mako na 21 a gasar Serie A da suka fafata ranar Asabar.

Cristiano Ronaldo wanda ya yi murnar cikarsa shekara 36 da haihuwa ranar Juma'a shi ne ya fara cin kwallo kuma a minti na 13 da fara tamaula, sannan Roma ta ci kanta na biyu

Kwallon da Ronaldo ya ci shi ne na 25 a kakar bana, bayan da ya buga wasa uku ba tare da ya zura kwallo a raga ba.

Kuma jumulla ya yi wasa 29 a kakar 2020/21 har ma ya karbi katin gargadi uku, sai dai kawo yanzu bai ci kwallo uku rigis a wasa ba.

Kyaftin din na Portugal shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Serie A mai 16 a raga, sai Romelu Lukaku da ke biye da shi mai 14.

Dan kwallon Juventus ya fara da zura kwallo biyu a raga a kakar bana a karawar da Portugal ta doke Sweden da ci 2-0 a Nations League.

Tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid wanda ya yi wasa 52 a kakar 2019/20 ya zura kwallo 48 a raga a dukkan fafatawa.

Nasarar da Juventus mai rike da kofin Italiya ta yi ya sa ta koma ta uku a gasar Serie A ta bana da maki 42.

Inter Milan ce ta daya a kan teburi da maki 47, sai AC Milan ta biyu mai maki 46.

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar Serie A:

  • Cristiano Ronaldo Juventus 16
  • Romelu Lukaku Inter Milan 14
  • Ciro Immobile Lazio 13
  • Zlatan Ibrahimovic AC Milan 12
  • Luis Muriel Atalanta 12
  • Joao Pedro Galvao Cagliari 11
  • Andrea Belotti Torino 11
  • Lautaro MartinezInter Milan 10