Paul Canoville: Bakar fatan da Chelsea ta soma dauka yana kwance a asibiti cikin matsanancin hali

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Tsohon dan kwallon Chelsea, Paul Canoville, na cikin matsanancin hali a asibiti, bayan da likitoci suka yi masa tiyata.
Canoville, mai shekara 58, shi ne bakar fada na farko da Chelsea ta dauka a 1981, ya kuma ci mata kwallo 15 a wasa 103.
Dan kwallon ya yi ritaya yana da shekara 25 da haihuwa, sakamakon rauni da ya yi a gwiwar kafa.
Conoville yana gudanar da gidauniyarsa wadda ke yaki da wariyar launin fata.
Tsohon dan wasan ya buga wa Reading tamaula ya kuma yi fama da ciwon cutar daji har karo uku.
Chelsea ta fitar da sanarwar cewa Paul yana cikin tarihinta, kuma ya fara buga mata kwallo a 1982, yayin da ya kasance "bakar fata na farko da ya fara buga mana tamaula."

Asalin hoton, Getty Images







