Andre Villas-Boas: Kocin Marseille ya mika takardar raba aurensa da kungiyar

An wallafa

Kocin Marseille Andre Villas-Boas ya ce ya bai wa mahukuntan kungiyar takardar neman izinin ajiye aiki saboda bai amince da tsarinta na "harkar tamaula" ba.

Kocin ya ce bai amince da kungiyar ta dauki Olivier Ntcham daga Celtic a lokacin cinikayyar 'yan kwallo cikin watan Janairu ba - wanda ya ce ba shi ne ya bayar da umarnin a dauke shi ba.

Kawo yanzu Merseille ba ta amince da takardar barin aiki da kocin ya mika mata ba.

Villas-Boas wanda ya koma horar da tamaula a Faransa a 2019 ya kara da cewar "ba na bukatar duk wani abu daga Marseille. Ba na bukatar wani kudin da za su ba ni."

Kan daukar Ntcham ya ce: "An dauki dan kwallo a cikin watan Janairu, kuma hukunci ne da ba ni ne na dauka ba, ban san komai kan batun ba."

"Ni kaina sai ji na yi a kafar yada labarai. Kuma dan wasan ne da ba ya cikin wadanda muke son dauka a jerin wadanda muke bibiyar tamaularsu."

Wannan batun ya bullo ne bayan kwana uku da aka soke karawar Marseille da Rennes, bayan tarzomar da ta barke a wajen atisaye.

'Yan sanda sun ce magoya bayan Marseille 300 ne suka kai musu hari a lokacin atisaye ranar Asabar.

Marseille tana ta tara a teburin Ligue 1 na Faransa, an kuma fitar da ita a gasar Champions League ta bana tun daga karawar cikin rukuni.