Kalubalen da Real Madrid za ta fuskanta a watan Fabrairu

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta fuskanci kalubale a wata Fabrairu, wadda za ta yi wasa shida har da daya a Champions League a bana.
Real Madrid ta kai zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai, sai dai tana ta uku a teburin La Liga da maki 40 iri daya da wanda Barcelona keda shi ta biyu a teburi.
Atletico Madrid ce ta daya mai kwantan wasa daya da tazarar maki 10 tsakaninta da Barcelona da Real Madrid.
A cikin watan Janairu aka fitar da Real Madrid daga Spanish Super Cup da kuma Copa del Rey na bana.
Saboda haka ya zama wajibi Real ta saka kwazo a watan na Fabrairu, idan ba haka ba ta fuskanci kakar bana ba tare da ta lashe kofi ba.
Real za ta fara wasan farko cikin watan Fabrairu ranar Asabar, inda za ta ziyarci Huesca domin buga gasar La Liga.
Kwana uku tsakani Real Madrid za ta karbi bakuncin Getafe a kwantan wasan tun na makon farko da basu buga ba.
A dai makon wato ranar Lahadi Real Madrid za ta buga gasar La Liga a gida da Valencia a filinta na Di Stefano.
Daga nan ne Real za ta ziyarci Real Valladolid a gasar La Liga ranar Lahadi 21 ga watan na Fabrairu.
Real Madrid za ta ziyarci Atalanta domin buga wasan farko a zagaye na biyu a gasar Champions League ranar Laraba 24 ga wata.
Real din za ta ƙarƙare watan Janairu da gasar La Liga da za ta karbi bakuncin Real Sociedad.
Wasannin da Real Madrid za ta kara a Fabrairu:
Ranar Asabar 6 ga watan Fabrairu La Liga
Huesca da Real Madrid
Ranar Talata 9 ga watan Fabrairu La Liga
Real Madrid da Getafe
Ranar Lahadi 14 ga watan Fabrairu La Liga
Real Madrid da Valencia
Ranar Lahadi 21 ga watan Fabrairu La Liga
Valladolid da Real Madrid
Ranar Laraba 24 ga watan Fabrairu Champions League
Atalanta da Real Madrid
Ranar Lahadi 28 ga watan Fabrairu La Liga
Real Madrid da Sociedad









