Joel Matip ba zai ci gaba da taka leda a kakar bana ba

Asalin hoton, PA Media
Ɗan wasan baya na Liverpool Joel Matip ba zai ci gaba da taka leda a kakar wasannin ta bana ba sakamakon rauni da ya ji a sawunsa.
Tsohon ɗan wasan na Kamaru mai shekara 29 ya samu raunin ne a wasan da suka tashi 3-1 da Tottenham ranar Alhamis ɗin da ta gabata.
Zai kasance da Virgil van Fijk da Joe Gomez a gefe, duk da cewa Liverpool ta ƙaro ƴan tsaron gida Ben Davies da Ozan Kabak.
Manajan ƙungiyar Jurgen Klopp ya ce: "Zai warke kafin fara kaka ta gaba, komai zai warware."
Klopp ya ce Matip - wanda ya samu raunin a lokacin da suka kara da Son Heung-min na Tottenham - ya ci gaba da buga tamaula duk da cewa bai da ƙoshin lafiya.
"Ba haka aka so ba saboda ya jajirce a wasan. Ya taimake mu a wasan da muka yi da Tottenham a lokacin da ya ƙwace ƙwallo da wurin Son.
"Amma ya samu rauni a sawunsa sannan ya ci gaba da buga wasan kuma yanzu an dakatar da shi a wannan kakar, don haka kun ga ya yi namijin ƙokari.
"Za mu jira shi. Yanzu yana da lokaci kafin ƙarshen wannan kakar, sannan ga lokacin bazara, ga kafin fara kaka ta gaba, duk zai shirya tsaf."









