Wane ne Tuchel sabon kocin Chelsea?

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Litinin Chelsea ta sallami Frank Lampard daga aikin kocin Chelsea.
Tsohon dan wasan kungiyar ya ja ragamar Chelsea wata 18, ya kuma bar Stamford Bridge kungiyar tana ta tara a teburin Premier League na bana.
Lampard ya zama na 12 da ya horar da Chelsea tun bayan da Roman Abramovic ya mallaki kungiyar a 2003.
Tuni dai ta sanar da ɗan kasar Jamus, Thomas Tuchel a matsayin wanda ya maye gurbinsa.
Shin wane ne Thomas Tuchel?
An haifi Thomas Tuchel ranar 29 ga watan Agustan 1973 a Krumbach, Jamus.
Mai tsaron baya ya fara taka leda a matashi a kungiyar TSV Krumbach 1979-1988 FC Augsburg 1988-1992
Ya ci gaba da wasa a matakin kwararren dan kwallo a Stuttgarter Kickers 1992-1994 SSV Ulm 1994-1998
Tuchel bai dade yana buga tamaula ba, sakamakon rauni da ya yi a gwiwarsa da ta kai ya yi murabus yana da shekara 25.
Daga nan ne ya fada sana'ar horar da kwallon kafa, wanda ya fara da karamar kungiyar Stuttgart.
Kungiyoyin da ya horar:
FC Augsburg II 2007-2008
Mainz 05 2009-2014
Borussia Dortmund 2015-2017
Paris Saint-Germain 2018-2020
Ya fara fito da kansa a 2009 lokacin da ya maye gurbin Jurgen Kloop a Mainz a gasar Bundesliga.
Shekara shida tsakanin ya kara maye gurbin Kloop a Borussia Dortmund a 2015.
Aikin da Tuchel ya yi ne a Dortmund ya sa aka san shi da kokarin da yake a fagen horar da kwallon kafa kuma matashi da ta kai Paris St Germain ta bashi aiki a 2018.
Bajintar da Tuchel ya yi a PSG:
Kocin ya ja ragamar Paris St Germain wasa 127, wanda ya yi nasara a karawa 95 da canjaras 13 aka doke shi fafatawa 19.
A lokacin da ya ja ragamar PSG ta ci kwallo 337 aka zura mata 103 a raga.
Kaka biyu da rabi da Tuchel ya yi a PSG ya taka rawar gani, wanda ya lashe kofi shida har da Ligue 1 biyu da Coupe de France da Coupe de la Ligue da kuma Trophees des Champions biyu a Faransa.
A kuma kakar 2019/20 ya kai PSG wasan karshe a Champions League, wanda Bayern Munich ta lashe.
Cikin watan Disamba aka salami Tuchel daga aiki a lokacin da PSG ke ta biyu a teburin gasar Faransa da tazarar maki daya tsakaninta da Lyon mai jan ragama.
Kwazon da Tuchel ya yi a Borussia Dortmund:
Kocin ya ja ragamar wasa 107 ya yi nasara a 67 da canajaras 23 aka doke shi sau 17.
A lokacinsa Dortmund ta ci kwallo 251 aka zura mata 115 a raga.
A kaka biyu da ya yi a Dortmund ya ci kofi daya DFB Pokal a shekarar 2017.
Ya kuma yin a biyu a gasar Bundesliga a kakar farko da ya ja ragamar kungiyar.
Ya kuma kai wasan quarter final a Europa League da kuma Champions League a Dotmund.
Wane salo Tuchel ke koyar da tamaula:
Kocin ya yi amfani da salon 4-3-3 a Dortmund da kuma PSG, idan ta kura masa yakan koma salon 3-5-2 ko kuma 5-3-2.
Kawo yanzu Tuchel idonsa ya bude a salon horar da kwallon kafa, har da gasar zakarun Turai da bait aba lashewa ba.
Duk kungiyar da ta dauke shi ya zama wajibi ta yi hakuri ta kuma bashi lokacin da zai samar da sakamakon da ake bukata.
Shin ko zai kai labari a gasar Premier League kuwa?
Gasar Premier tana cike da kalubale ta ko ina tun daga horarwa da yan wasa da wasannin hamayya a kowanne mako ga kuma cutar korona da ta maida hannun agogo baya.











