Kasuwar cinikin ‘yan kwallo: Makomar Lingard, Trippier, Balogun, Rose, Ozil, Garcia

Asalin hoton, Getty Images
Wakilan Jesse Lingard, dan wasan Ingila da Manchester United mai shekara 28 na tattaunawa da Nice kan bayar da aronsa cikin mako mai zuwa. (Sky Sports)
Kocin Newcastle Steve Bruce ba shi da matsala a wajen mai kungiyar Mike Ashley duk da yadda magoya bayan kungiyar ke ta kiraye-kirayen da a sallame shi bayan da Sheffield United ta doke kungiyar cikin makon nan. (Sky Sports)
Manchester United ta fasa dauko Kieran Trippier, dan wasan Atletico Madrid mai shekara 30 saboda rashin tabbaci kan hukunccin da aka yanke ma sa kan laifin da ya aikata na yin caca. (Manchester Evening News)
Tottenham na iya soke kwantiragin dan wasanta Danny Rose cikin wannan watan, inda ake sa ran West Brom ta bayyana sha'awar sayen dan wasan na baya na Ingila. (Talksport)
Dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil mai shekara 32 ya amince a rage ma sa albashinsa na fam miliyan 7 wanda za a biya shi a karshen kakar wasan nan saboda ya iya barin kungiyar a wannan watan. (The Athletic)
Dan wasan Manchester City da Spaniya Eric Garcia mai shekara 20 ya amaince da tayin da Barcelona ta yi ma sa, amma da sauran tattaunawa kafin ya tafi can. (Goal)
Kocin Barcelona Ronald Koeman ya na da karfin gwuiwa Georginio Wijnaldum, dan wasan Netherlands da Liverpool da Memphis Depay na Lyon za su koma kungiyar a kakar wasan nan. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Dan wasan gaba naArsenalFolarin Balogun, mai shekara 19 ya amince ya koma RB Liepzig. (Football Insider)
Liverpool na shirin dauko Ben White, dan wasan baya na Brighton mai shekara 23 a cikin wannan kakar wasan. (Liverpool Echo)
Celtic da Rangersna bukatar Taiwo Awoniyi, dan wasan Najeriya mai shekara 23, wanda a yanzu ke wasa a matsayin dan aro a Union Stade ta gasar Bundesliga. (90 Min)












