Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Bissouma, Giroud, Salah, Mbappe, Alaba
Manchester United na sha'awar dauko Yves Bissouma, dan wasan Brighton da Mali mai shekara 24 da Liverpool da Arsenal ma ke nema ruwa a jallo. (Express)
Marseille na sha'awar dauko Oliver Giroud, dan wasa mai shekara 34 na asalin kasar Faransa mai buga wasa a Chelsea. (le10sport - in French)
Liverpool na tunanin sayar da dan wasanta na gaba Mohamed salah mai shekara 28 saboda ba ya jin dadin zama a kungiyar, inji tsohon dan wasan Masar Mohamed Aboutrika. (Bein Sports via Goal)
Real Madrid na da karfin gwuiwar dauko dan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe mai shekara 22 daga Paris St-Germain a kakar wasa ta badi. (90 Min)
Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya amince wa dan wasan baya David Alaba mai shekara 28 ya bar kungiyar ta kasar Jamus, inda Real Madrid ce ake sa ran za ta dauke shi. (Marca)
Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester United na ganin kungiyar za ta iya zama babbar kishiyar Liverpool a gasar lashe kofin firimiyar bana. (Sky Sports)
Tsohon kocin West Brom, Slaven Bilic ya san kungiyar za ta kore shi yayin da yake cikin mota daga Manchester City a makon jiya. (Telegraph - subscription)
Kocin Juventus Andrea Pirlo ya ki tabbatar zai sayar da dan wasan gaba Paulo Dybala mai shekara 27. (Mail)
Manchester City a shirye ta ke ta saurari masu son sayen dan wasan bayanta Oleksandr Zinchenko mai shekara 24 da zarar an bude kasuwa a watan Janairu. (Express)
Dan wasan baya na Chelsea da Jamus Antonio Rudiger mai shekara 27 ya yarda cewa bai gamsu da halin da yake ciki ba a kungiyar, amma ya ce ba zai nemi komawa wata kungiyar ba a watan Janairu. (ZDF via Mail)