Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon kafar zinare na 2020

An wallafa

Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon kafar zinare na 2020, wadda ake karrama 'yan wasan tamaula da suka haura shekara 28 suka kuma yi fice a duniya.

Tun ranar daya ga watan Disamba aka sanar da Ronaldo mai shekara 35 shi ne ya zama zakaran bana, amma sai yanzu aka mika masa kyautar.

Wannan ne karo na 18 da ake bayyana kyautar gwarzon kafar zinare, kuma karon farko da dan kasar Portugal ya zama gwani.

A zaben da aka gudanar domin fitar da gwanin shekarar nan, Ronaldo ya yi takara ne da Lionel Messi da Robert Lewandowski da Giorgio Chiellini da Neymar da kuma Sergio Ramos.

Sauran sun hada da Sergio Aguero da Gerard Pique da Mohamed Salah da kuma Arturo Vidal.

A makon jiya ne Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na 2020 na Fifa na duniya.

Dan kasar Poland ya yi takara ne da Cristiano Ronaldo na Juventus da dan kwallon Barcelona Lionel Messi.

Kyaftin din Argentina, Messi bai taba lashe kyautar gwarzon kafar zinare ba a tarihi.

Ga jerin wadanda suka lashe kyauta 17 a baya:

  • Roberto Baggio (2003)
  • Pavel Nevded (2004)
  • Andriy Shevchenko (2005)
  • Ronaldo Nazario (2006)
  • Alessandro Del Piero (2007)
  • Roberto Carlos (2008)
  • Ronaldinho (2009)
  • Francesco Totti (2010)
  • Ryan Giggs (2011)
  • Zlatan Ibrahimovic (2012)
  • Didier Drogba (2013)
  • Andres Iniesta (2014)
  • Samuel Eto'o (2015)
  • Gianluigi Buffon (2016))
  • Iker Casillas (2017)
  • Edinson Cavani (2018)
  • Luka Modric (2019)