Real ta koma ta biyu a teburin La Liga, bayan doke Eibar

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid ta koma ta biyu a kan teburin La Liga, bayan da ta je ta doke Eibar da ci 3-1 a wasan mako na 14 a gasar La Liga ranar Lahadi.
Karim Benzema ne ya fara ci wa Real Kwallo a minti na shida da fara tamaula, sannan minti bakwai tsakani Luka Modric ya kara na biyu.
Eibar ta zare kwallo daya ne ta hannun Kike Garcia a minti na 28 da take leda.
Daf da za a tashi daga gumurzun ne Real Madrid ta kara na uku ta hannun Lucas Vazquez da hakan ya tabbatar mata da maki ukun da take bukara.
Cikin wasa 14 da ta buga a bana ta yi nasara a tara da canjaras biyu da rashin nasara a karawa uku.
Haka kuma Real mai rike da kofin ta ci kwallo 25 aka zura mata 14 a raga, saura wasa 24 a La Liga da ke gaban kungiyar a bana.
Da wannan sakamakon Real ta koma ta biyu da maki 29 iri daya da na Atletico Madrid wadda ke jan ragamar teburin La Liga.
Kafin karawar Real Madrid tana mataki na uku a kan teburi da maki 26, ita Eibar mai maki 15 tana ta 13 a kasan teburin gasar bana.
A kakar bara da kungiyoyin biyu suka fafata a La Liga:
- Lahadi 14 ga watan Yunin 2019 Real Madrid 3 - 1 Eibar
- Asabar 9 ga watan Nuwambar 2019 Eibar 0 - 4 Real Madrid
'Yan wasan 22 da Zinedine Zidane ya je da su Eibar.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da E. Militão da Sergio Ramos da R. Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Odegaard.
Masu cin kwallaye: Benzema da Asensio da Lucas V. da Jovic da Mariano da kuma Rodrygo.










