Halin da Sheikh Lukuwa ke ciki bayan matashi ya caka masa wuƙa a masallaci

Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa Sokoto

Asalin hoton, Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa Sokoto/FB

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

An shiga cikin fargaba a birnin Sakkwato ranar Juma'a bayan da wani matashi ya daɓa wa wani malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Lukwa, jim kaɗan bayan ya jagoranci sallar Juma'a a masallacinsa da ke unguwar Mabera a birnin Sokoto.

Rahotanni sun ce matashin na cikin masu ibadar da suka halarci sallar, inda ake zargin ya caka masa wuƙa sau biyu a wuya, lamarin da ya nan da nan aka garzaya da shi asibiti.

Wani bidiyo da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook, jim kaɗan bayan sallamarsa daga asibitin ya nuna wuyansa ɗaure da bandeji, inda yake kiran magoya bayansa su kwantar da hankali.

''Jama'a kowa ya kwantar da hankalisa, ina cikin ƙoshin lafiya, babu wata matsala, lafiyar ƙalau nake ban jin komai ga jikina, Allah ya bani kariya'', kamar yadda ya bayyana a cikin bidiyon mai tsawo sakan 32.

Jaridar Daily Trust ta ambato wasu majiyoyi na cewa wanda ake zargin yana zaune ne tare da sauran masu ibada a cikin masallacin, har ma a sahun gaba, kafin ya afka wa malamin nan take bayan an kammala sallar.

Rahotanni sun danganta lamarin da wani wa'azi da Malam Musa Lukwa ya gabatar a baya, inda ya kawo wani hadisi da wasu malaman addini, musamman masu alaƙa da ɗariƙa, suka ɗauka a matsayin abin taɓa martabar iyayen Annabi Muhammad (SAW).

Tun d afarko dai wasu ƙungiyoyin Malaman addinin Musulunci da suka haɗa da na ƙungiyar sufaye ta Tijjaniya a Najeriya da zuri'ar Sheikh Usmanu Danfodiyo da sauran su, sun gabatar da koke ga gwamnatin Jihar Sakkwato da kuma Fadar Mai alfarmaSarkin Musulmi kan wasu kalamai da ake dangantawa da Sheikh Ayyuba Musa Lukuwa da ake zargi suna taɓa martaba da matsayin Annabi Muhammad (SAW).

Tawagar ta miƙa koken ga hukumomin da abin ya shafa, tana kira da a ɗauki matakin gaggawa.

Malam sun ce kalaman na iya tayar da fitina da kuma barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'ummar Muslumi.

Da me ake zargin Sheikh Lukuwa?

Shugaban Majalisar Sufaye a Najeriya, wadda ke wakiltar mabiya ɗarikun Tijjaniyya da Qadiriyya, Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal ya bayyana cewa kalaman da ake zargin an yi sun kasance abin ƙyama kuma ba za a amince da su ba.

"Yana cewa mahaifan annabi Muhammad suna cikin azaba kuma yana ta nanatawa kamar da gangan ake yi domin a tashi hankalin Musulmi," in ji Farfesa Yagawal.

Farfesa Abubakar ya kuma ƙara da cewa zarge-zargen sun hada da cin mutumcin Shehu Usmanu Danfodio da ma Fadar Sarkin Musulmi.

"Yana kuma zagin mutane masu mutumci. Yana zagin Sarkin Musulmi. Da kuma kiran a rushe hubbaren Shehu a mayar da shi filin ƙwallo. Da kwatanta kabarin Shehu da na Ojukwu duk ɗaya .

"Wannan cin zarafi da yake yi wa annabi Muhammad SAW wanda duk Musulmi mai imani ba zai ji daɗin hakan ba kuma ba zai kasa yin wani abu ba idan har yana iya yi. Ya daɗe yana cin zarafin annabi,"

Martanin Sheikh Lukuwa

To sai dai Sheikh Ayuba Musa Lukuwa ya ce an yi wa kalamansa bahaguwar fahimta, domin kuwa duk abubuwan da ya faɗa ya tsamo su ne daga hadisai da tarin hujjoji.

Ya kuma nemi a zauna tsakaninsa da malaman domin yin muƙabala kan batutuwan da suke zargin sa da su.

"Yau kwana shida da muka rubuta musu...ta neman muƙabala domin mu zauna da su mu yi karatu a kan waɗannan matsaloli...a dauki litattafan addini a yi karatu mu kuma nuna inda muka waɗannan abubuwan...shin ga manzon Allah na samo su ko kuma ni ne na ƙirƙiro su.

Mun kai wasiƙar ma'aikatar lamuran addinin sannan mun kai ta fadar Sarkin Musulmi kuma mun kai wa kwamishinan ƴansanda," in ji Sheikh Lukuwa.

Wane ne Sheikh Musa Lukuwa?

..

Asalin hoton, Sheikh Lukuwa/Facebook

Malam Musa Ayuba Lukuwa malamin addinin Musulunci ne a jihar Sokoto da ke bin fahimtar Ahlussunnah Wal Jama'a.

Yana daga cikin malamai masu yawan janyo taƙaddama musamman dangane da al'amura masu sarƙaƙiya.

Ya shahara wajen ra'ayoyi masu cin gashin kansu kan fikihun Musulunci da wasu ayyukan ibada.

Misali, game da tabbatar da ganin jinjirin wata na bukukuwan Musulunci irin su Idi, ya kasance yana jaddada muhimmancin dogaro da ganin watan a cikin gida ko yankin da ke kusa, kamar a Jamhuriyar Nijar maƙwabciya, maimakon jingina gaba ɗaya ga sanarwar da ta fito daga wurare masu nisa kamar Saudiyya.

A baya-bayan nan hotuna da bidiyo na kafar sada zumunta sun nuna malamin mai tarun shekaru ɗauke da bindiga biyo bayan barazanar da ya fuskanta bisa zargin taɓa ƙimar annabi Muhammad SAW.