Ronaldo ya barar da fenariti a karawa da Atalanta

Asalin hoton, Getty Images
Juventus ta tashi wasa 1-1 da Atalanta a gasar cin kofin Serie A da suka kara ranar Laraba.
Wannan shi ne wasa na shida da mai rike da kofi, Juventus ta yi canjaras a bana, bayan buga karawar mako na 12 a gasar.
Federico Chiesa ne ya fara ci wa Juventus kwallo mai kayatarwa daga wajen da'ira, kuma na farko da ya ci wa Juventus a lik.
Atalanta ta farke kwallo ta hannun Remo Freuler da hakan ya sa suka raba maki a tsakaninsu.
Cristino Ronaldo ya buga fenariti, amma mai tsaron raga Pierluigi Gollini ya tare kwallon.
Ronaldo ya samu damar kara na biyu, amma dai kwallo bai shiga ragar Atalanta ba.
Tsohon golan Aston Villa, Gollini ya taka rawar gani a karawar, har ma ya hana kwallon da Alvaro Morata ya buga masa shiga raga.
Juventus wadda ta lashe kofin Serie A tara - ba a doke ta ba a wasa 12 karkashin jagorancin Andrea Pirlo a bana - koda yake rabin wasannin canjaras ta yi.
Kungiyar tana ta uku a kan teburi da tazarar maki uku tsakaninta da AC Milan mai jan ragama.











