Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Williams, Bale, Marcelo, Eriksen, Saliba, Small, Dybala, Van de Beek

An wallafa

Southampton na son karbar aron dan wasan Manchester United dan kasar Ingila Brandon Williams, mai shekara 20, a watan Janairu. (Telegraph)

Dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 31, yana son taka rawar gani a kakar wasa mai zuwa a Real Madrid bayan zaman aronsa a Tottenham. (AS)

West Ham za ta iya daukar dan wasan Lyon dan kasar Brazil Marcelo, mai shekara 33, a kakar wasa mai zuwa. (Sun)

Dan wasan Inter Milan dan kasar Denmark Christian Eriksen, mai shekara 28, ya shirya yin watsi da batun komawa Premier League sannan ya nuna turjiya ga batun tafiya Paris St-Germain. (Star)

Dan wasan Arsenal dan kasar Faransa William Saliba, mai shekara 19, yana son tafiya zaman aro a wata kungiyar a Ingila maimakon komawa Faransa a watan Janairu. (The Athletic - subscription only)

Everton na da kwarin gwiwar rike dan wasan Ingila Thierry Small duk da rahotannin da ke cewa dan wasan mai shekara 16 zai tafi Arsenal, Bayern Munich ko kumaJuventus. (Liverpool Echo)

Shugaban Juventus Andrea Agnelli ya ce kungiyar ta bukaci tsawaita zaman dan wasan Argentina Paulo Dybala bayan dan wasan mai shekara 27 ya yi ikirarin cewa ba a nemi sabunta kwangilarsa ba. (Tuttosport via Football Italia)

Dan wasan Watford Troy Deeney ya ce dole kocin Arsenal Mikel Arteta ya gudanar da taro da 'yan wasansa bayan kungiyar ta sha kashi a hannun Burnley a karshen makon jiya. (Talksport)

Tsohon dan wasan Leeds Noel Whelan ya ce dan wasan kungiyar dan kasar Portugal Helder Costa "bai tabuka komai ba" bayan an koma daga hutun rabin lokaci a wasan da West Ham ta doke su da ci 2-1. (Football Insider)

Tsohon dan wasan Netherlands Johnny Heitinga ya bayana shakkunsa kan zabin da dan kasarsa mai shekara 23 Donny van de Beek ya yi na tafiya Manchester United. (Stadium Astro via Mirror)