Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasan Real 20 da za su fafata da Athletic Bilbao a gasar La Liga
Real Madrid za ta karbi bakuncin Athletic Bilbao a gasar cin kofin La Liga ranar Talata a filinta na Alfredo Di Stéfano.
Tun farko wannan wasan kamata ya yi a buga shi a mako na 19, amma aka dawo da shi ranar Talata.
Ranar Litinin 15 ga watan Disamba za a karkare karawar mako na 13 a gasar ta Spaniya.
Bayan da Real ta koma kan ganiya za ta buga wasanne ba tare da mai buga mata tsakiya ba Casemiro, sakamakon hukuncin dakatarwa.
A karawar hamayya da Real ta yi da Atletico Madrid da ta yi nasara da ci 2-0 ranar Asabar, ta yi amfani da masu buga mata tsakiya wato Casemiro da Toni Kroos da kuma Luka Modric.
Watakila Real ta bai wa 'yan wasa dama kamar Isco da kuma Marco Asensio a karawar La Liga ranar Talata da Athletic Club din.
Real Madrid ta buga atisaye ranar Litinin ba tare da 'yan wasa da suka hada da Eden Hazard da Mariano Diaz da Martin Odegaard da kuma Luka Jovic.
Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasan Real Madrid 20 da zai fuskanci Athletic Bilbao da su.
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carvajal da E. Militão da Sergio Ramos da R. Varane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos da Modrić da Valverde da kuma Isco.
Masu cin kwallaye: Benzema da Asensio da Lucas V. da Vini Jr. da kuma Rodrygo.