Diogo Jota ya zama na bakwai da ke jinya a Liverpool

An wallafa

Dan wasan Liverpool, Diogo Jota zai yi jinyar mako shida, sakamakon raunin da ya ji a karawar Champions League.

Dan kwallon tawagar Portugal ya yi rauni ne a wasa da Midtjylland a lokacin Gasar Champions League ranar Laraba.

''Raunin ya munana fiye da yadda muka dauka tun farko,'' in ji kocin Liverpool Jurgen Klopp a hira da Sky Sports.

"Mun yi tsammanin sai likitoci sun yi masa tiyata, sai dai kuma ba a bukatar hakan. Illa dai zai yi jinya. Ba tabbacin kwanakin jinya.''

Kawo yanzu Jota ya ci wa Liverpool kwallo tara, tun bayan da ya koma Anfield da murza leda daga Wolverhampton cikin watan Satumba.

Dan wasa ya zama na bakwai a jerin 'yan kwallon Liverpool da ke jinya da suka hada da Virgil van Dijk da Joe Gomez da kuma Konstantinos Tsimikas.

Sauran da ke yin jinya sun hada da James Milner da Thiago Alcantara da kuma Xherdan Shaqiri.

Sai dai kuma mai tsaron raga Alisson da Alex Oxlade-Chamberlain sun warke, har ma sun yi zaman benci a wasan da Liverpool ta tashi 1-1 da Fulham ranar Lahadi a gasar Premier League.