Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me kuke son sani kan jadawalin Champions League ranar Litinin?
Ranar Litinin 14 ga watan Disamba za a raba jadawalin kungiyoyi 16 a gasar Champions League da za a yi a birnin Nyon, Switzerland.
Wadanda suka ja ragamar rukuni: Bayern Munich da Chelsea da Dortmund da Juventus da Liverpool da Manchester City da Paris St Germain da kuma Real Madrid.
Wadanda suka yi na biyu a rukuni: Atalanta da Atletico Madrid da Barcelona da Lazio da RB Leipzig da Borussia Mönchengladbach da FC Porto da kuma Sevilla.
Za a fara wasannin zagaye na biyu na kungiyoyi 16 karawar farko tsakanin 16 da 17 da 23 da kuma 24 ga watan Fabrairu.
Za kuma a buga wasa na biyu ne ranar 9 da 10 da 16 da kuma 17 ga watan Maris
Ga yadda kungiyoyin za su tantance wadanda za su iya haduwa a karawar zagaye na biyu a Champions League na 2020/21.
Wadanda suka yi na daya a rukuni
Bayern Munich Jamus
Wadanda za ta iya haduwa da su: Atalanta ko Barcelona ko Lazio ko Porto ko kuma Sevilla.
Chelsea Ingila
Wadanda za ta iya haduwa da su: Atalanta ko Atlético ko Barcelona ko Lazio ko Leipzig ko Mönchengladbach ko kuma Porto.
Borussia Dortmund Jamus
Wadanda za ta iya haduwa da su: Atalanta ko Atlético ko Barcelona ko Porto ko kuma Sevilla
Juventus Italiya
Wadanda za ta iya haduwa da su: Atlético ko Leipzig ko Mönchengladbach ko Porto ko kuma Sevilla
Liverpool Ingila
Wadanda za ta iya haduwa da su: Atlético, Barcelona, Lazio, Leipzig, Mönchengladbach, Porto, Sevilla
Manchester City Ingila
Wadanda za ta iya haduwa da su: Atlético ko Barcelona ko Lazio ko Leipzig ko Mönchengladbach ko Sevilla
Paris St Germain
Wadanda za ta iya haduwa da su: Atalanta, Atletico, Barcelona, Lazio, Mönchengladbach, Porto, Sevilla
Real Madrid Spaniya
Wadanda za ta iya haduwa da su:: Atalanta ko Lazio ko Leipzig ko kuma Porto
Wadanda suka yi na biyu a rukuni
Atalanta Italiya
Wadanda za ta iya haduwa da su: Bayern, Chelsea, Dortmund, Man. City, Paris, Real Madrid
Atlético Madrid Spaniya
Wadanda za ta iya haduwa da su: Chelsea ko Dortmund ko Juventus ko Liverpool ko Manchester City ko kuma, Paris St Germain
Barcelona Spaniya
Wadanda za ta iya haduwa da su: Bayern Munich ko Chelsea ko Dortmund da Liverpool ko Manchester City ko kuma Paris St Germain
Lazio Italiya
Wadanda za ta iya haduwa da su: Bayern Munich ko Chelsea ko Liverpool ko Manchester City ko Paris St Germain ko kuma Real Madrid
Leipzig Jamus
Wadanda za ta iya haduwa da su: Chelsea ko Juventus ko Liverpool ko Manchester City ko kuma Real Madrid
Mönchengladbach Jamus
Wadanda za ta iya haduwa da su: Chelsea ko Juventus ko Liverpool ko Manchester City ko kuma Paris St Germain
Porto Portugal
Wadanda za ta iya haduwa da su: Bayern Munich ko Chelsea ko Dortmund ko Juventus ko Liverpool ko Paris St Germain ko kuma Real Madrid
Sevilla Spaniya
Wadanda za ta iya haduwa da su: Bayern Munich ko Dortmund ko Juventus ko Liverpool ko Manchester City ko kuma Paris St Germain