Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Pogba, Haaland, Mbappe, Alli, Kepa, Saliba
Dan wasan Faransa Kylian Mbappe mai shekara 21 ya ce sai iyayensa sun amince kafin ya iya barin Paris St-Germain zuwa wata kungiyar. (Copa 90 via Sun)
Juventus da Manchester United za su kyale dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba mai shekara 27 ya koma Turin a watan gobe a matsayin dan aro. (Mirror)
Tuni Manchester United ta yi watsi da wata bukata ta Douglas Costa mai shekara 30 ya koma Juventus, da kuma Miralem Pjanic dan kasar Bosnia mai shekara 30 ya baro Barcelona a madadin Pogba. (Calciomercato)
Mahaifin Erling Braut Haaland wato Alf Inge ya ce dan wasan mai shekara 20 na jin dadin zaman da yake yi a Borussia Dortmund a yanzu, amma yana iya komawa wata kungiyar nan gaba. (Tuttosport via Goal)
Shugaban Tottenham Daniel Levy na iya amincewa Dele Alli, dan wasan tsakiya mai shekara 24 ya koma Paris St. Germain a matsayin dan wasan aro na wata 18. (90min)
Chelsea na fuskantar matsalar rabuwa da gola Kepa Arrizabalaga dan wasa mai shekara 26, da Marcos Alonso mai shekara 29 da dan wasan baya Andreas Christensen mai shekara 24. (Express)
Wolves are considering a move for 17-year-old Mainz midfielder Marlon Roos-Trujillo, who has represented Germany at under-19s level
Wolves na tunanin sayo Marlon Roos-Trujillo dan wasan tsakiya na Mainz mai shekara 17. Dan wasan ya wakilci Jamus a kungiyarsu ta 'yan kasa da shekau 19 . (Bild)
West Brom ta kosa ta sayo Dwight Gayle, dan wasan Ingila mai shekara 30 daga Newcastle tun da kwantiraginsa za ta kare a karshen kakar wasa ta bana. (Birmingham Live)
Arsenal na daf da sayar da William Saliba, dan wasan Faransa mai shekara 19 nan da watan Janairu ga duk mai bukata saboda ba ta ganin za ta yi amfani da shi a gasar Firimiyar Ingila. (Football London)
Kocin Middlesbrough Neil Warnock na bukatar Duncan Watmore, dan wasan Ingila mai shekara 26 ya sabunta kwantiraginsa da kungiyar, ganin cewa wasu kungiyoyin na son dauke shi. (Sun)