Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real ba za ta kara da kungiyar Spaniya a zagaye na biyu ba
Gasar Champions Legue ta shekarar nan ta koma kungiyoyi 16 daga 32 da suka buga karawar rukuni a wasannin 2020/21.
Hakan na nufin an samu wadanda za su buga zagaye na biyu kenan, da za a raba jadawali ranar Litinin.
Kungiyoyin Spaniya hudu ne suka kai karawar gaba, bayan da Real Madrid ta ja ragamar rukuni na biyu.
Sauran kungiyoyin Spaniya sun kai zagaye na biyu ne a mataki na bibiyu a rukunansu da ya hada da Barcelona da Atletico Madrid da kuma Sevilla,
Real Madrid wadda ta yi ta daya a rukuninta na nufin ba za ta hadu da Bayern Munich ko Manchester City ko Liverpool ko Juventus ko Paris Saint-Germain ko Chelsea ko kuma Borussia Dortmund a wasan zagaye na biyu ba..
Wasu na hangen Chelsea da Dortmund sune marasa karfi sosai da suka ja ragamar rukuninsu, amma ana hasashen sauran kungiyoyi uku na La Liga za su iya haduwa da kungiyoyi masu zafi a karawar zagayen gaba.
Watakila Real Madrid ta hadu da kungiya mai sauki a zagaye na biyu, bayan da ta yi ta daya a rukuni na biyu.
Sai dai babu yadda Real za ta hadu da Borussia Monchengladbach wadda suka yi wasa daya tare a rukuni da kuma kungiyoyin Spaniya a karawar zagaye na biyu.
Kungiyoyi da dama ba za su so haduwa da RB Leipzig wadda ta kai wasan daf da karshe a bara ko kuma Lazio, domin za su yi wahalar dokewa.
Atalanta tana daga cikin wadanda keda matasa masu zafi, kamar yadda ta ci wasa a bana a Anfield da Amsterdam, duk inda ta je bata da fargaba.
Kungiyar Porto ce ake hange mai dan sauki, kuma Real Madrid za ta iya haduwa da ita, amma a harkar kwallon kafa sai an tashi.