Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Hudson-Odoi, Haaland, Szoboszlai, Messi, Grealish, Wijnaldum

Asalin hoton, Getty Images
Bayern za ta yi hakuri har sai Hudson-Odoi, dan wasa Chelsea ya shiga hannunta idan aka bude kasuwar cinikin 'yan wasa a watan Janairu, amma Zakarun na Turai za su ci gaba da sa ido kan dan wasan mai shekara 20 kuma dan Ingila ya shiga kasuwa. (Goal)
Manchester City da Manchester United na daf da bayyana sha'awarsu ta daukan Erling Braut Haaland, dan wasan Borussia Dortmund mai shekara 20 a watanni ma su zuwa. (Mail)
Dan waasan tsakiya na Red Bull Salzburg's kuma dan kasar Hungary Dominik Szoboszlai, wanda ke da shekara 20, ya ce ba zai amince ya koma Arsenal ba, sai dai yana son komawa RB Leipzig a watan Janairu. (Sky Germany via Sky Sports)
Kocin Leicester Brendan Rodgers ya sanar da Demarai Gray, dan wasan Ingila a ajin 'yan kasa da shekara 21, cewa ba a bukatar sa a kungiyar da aka fi sani da Foxes. (Mail)
Dan wasan tsakiya na Atletico Madrid Koke, mai shekara 28 ya bayyana yadda zai so ya lallashi Lionel Messi domin ya koma kungiyarsa daga Barcelona, amma ya ce abu ne mai matukar wuya ya iya barin Barca. (As)
Kocin Barcelona Ronald Koeman yana kan bakarsa ta dauko Georginio Wijnaldum, dan wasan tsakiya mai shekara 30 kuma dan kasaar Netherlands, daga Liverpool. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Dan wasan Uruguay Edinson Cavani mai shekara 33 sai da ya juya wa Juventus da Inter Milan baya domin ya sami damar komawa Manchester United. (Sun)
Leicester da West Ham na sa ido kan Amadou Diawara dan wasan ma shekara 23 kuma dan kasar Guinea idan Roma za ta sayar da shi. (Leicester Mercury)
Dan wasan gefe na Leeds Raphinha, mai shekara 23 kuma dan Brazil ya ce bai ji dadin yadda Rennes ta yanke shawarar sayar da shi ba zuwa Gasar Firimiyar Ingila ba tare da ta tuntube shi ba. (ESPN Brazil via Goal)
Tsohon dan wasan Arsenal Louis Saha na ganin da kungiyar za ta sake dauko Olivier Giroud, dan wasan gaba mai shekara 34 daga Chelsea a watan Janairu da abin ya yi mata kyau kuwa. (Metro)











