Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar White, Upamecano, Alaba, Garcia, Rojo, Eriksen, Szoboszlai

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta saka Ben White, dan wasan Brighton da Ingila mai shekara 23 cikin masu tsare wa kungiyar baya da ta ke son sayowa. Akwai kuma Dayot Upamecano na RB Leipzig da Raphael Varane na Real Madrid. (MEN)
Paris St-Germain na shirin karbo aron Dele Alli, dan wasan tsakiya mai shekara 24 na Tottenham kuma sun yi imani ƙungiyar Spurs a shirye ta ke ta sake shi. (Mail)
Idan Chelsea na son sayen David Alaba, dan wasan Bayern Munich mai shekara 28, to dole ta biya shi albashin da yafi na sauran ƴan wasan ƙungiyar. (Mirror)
Kocin Arsenal Mikel Arteta na son sayo Eric Garcia, dan wasan baya na Sfaniya mai shekara 19 daga Manchester City. (Sun)
Yawan albashin Christian Eriksen, dan wasan Denmark a ƙungiyarsa ta Inter Milan na iya hani shi komawa Gasar Firimiyar Ingila saboda zai yi wa ƙungiyoyi tsada matuƙa. (Telegraph - subscription required)
Ficewar Red Bull Salzburg daga gasar Zakarun Turai ya ba Arsenal damar sayo Dominik Szoboszlai, ɗan wasan Hungary mai shekara 20 a watan Janairu. (Football.London)
Arteta na fatan Folarin Balogun, dan wasan gaba mai shekara 19 zai ci gaba da zama a ƙungiyar Arsenal. Kwantiragin dan wasan za ta ƙare a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Metro)
West Brom ta fara neman ƴan wasan da za su maye gurbin kocin ƙungiyar Slaven Bilic wanda za a iya kora idan Newcastle ta doke ta ranar Asabar. (Mail)
Shugaban Bayern Munich Karl-Heinz Rummenigge ya ce ƙungiyar ba ta buƙatar sayo Erling Braut Haaland, dan wasan gaba mai shekara 20 na Borussia Dortmund da Norway, domin suna da Robert Lewandowski, mai shekara 32. (Tuttosport - in Italian)
Tsohon dan wasan Netherlands da Arsenal, Robin van Persie ya ce ya taba gaya wa kocin ƙungiyar na da Arsene Wenger ya sayo Giorgio Chiellini, dan wasa mai shekara 36 domin zai taimaka wa ƙungiyar ta lashe gasar firimiyar Ingila. (Effe Relativing, via Metro)










