Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: Abin da Madrid da Man United ke buƙata kafin su je zagaye na gaba
Rukunin H na Real Madrid da Inter Milan da Borussia Monchengladbach da Shakhtar na cikin halin fargaba, sakamakon kowannensu na da damar zuwa zagaye na gaba a wasan ƙarshe.
Monchengladbach za ta ziyarci Real Madrid a yau. Duk wanda ya ci wasa a cikinsu shi ne zai fito daga rukunin. Haka nan idan aka yi canjaras Monchengladbach ce za ta fito.
Real Madrid za ta iya fitowa idan aka yi canjaras amma dole ne sai Inter ta doke Shakhtar. Hakan zai faru ne saboda Madrid ta fi zira wa Inter ƙwallaye - ba Shakhtar ba.
Idan Shakhtar ta ci wasa za ta fito. Kuma za ta iya fitowa ma da canjaras indai Madrid ta ci nata wasan.
Wajibi ne Inter Milan ta ci wasa kafin ta fito. Ko da ta ci, indai aka tashi canjaras a ɗaya wasan to gida za ta koma.
Manchester United
Rukunin H da ya ƙunshi Manchester United da PSG da RB Leipzig da Istanbul Basaksehir, shi ma a rikice yake.
Man United na buƙatar maki ɗaya kacal domin ta samu zuwa zagaye na gaba. Idan har aka doke ta a wasa tsakaninta da RB Leipzig to za ta wuce kai tsaye zuwa Europa League.
Za ta ƙare a mataki na ɗaya a rukunin (idan PSG ba ta ci Istanbul Basaksehir ba), idan PSG ta ci wasanta, ita ce za ta jagoranci rukunin ko da kuwa Man United ta ci wasa.
Leipzig za ta wuce zagaye na gaba idan ta ci wasa. Idan kuma ta yi canjaras to za ta buƙaci a cinye PSG.
Idan PSG da Man United suka yi rashin nasara PSG ce za ta fito (tare da Leipzig) saboda bambancin yawan ƙwallayen da PSG ta ɗura wa United.