Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Lingard, Ozil, Kepa, Vazquez, Romero, Fabinho

An wallafa

Wakilan Jesse Lingard suna duba yiwuwar tura dan wasan Manchester United da Ingila wata kungiyar domin yin zaman aro a watan Janairu, kuma rahotanni sun ce sun tattauna da Real Sociedad a kan makomar dan wasan mai shekara 27. (Sky Sports)

Dan wasan Arsenal dan kasar Jamus da ba a damawa da shi Mesut Ozil, mai shekara 32, ya yanke shawarar tafiya Fenerbahce a watan gobe, a cewar wasu 'yan majalisar dokokin Turkiyya. (Sport Digitale, via Mirror)

Kocin Chelsea Frank Lampard ya ce ba ya fuskantar matsin lamba domin ya sayar da golan Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 26, wanda suka saya a kan £71m. (Evening Standard)

Manchester United za ta mayar da hankali kan dan wasan Real Madrid dan kasar Sifaniya Lucas Vazquez, mai shekara 29, a yayin da take neman wanda zai rika zama a gurbin dan wasan Ingila Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 23. (Defensa Central - in Spanish)

Kazalika United za ta bar golan Argentina Sergio Romero ya bar kungiyar a watan gobe ba kuma za ta sayar da shi idan aka taya shi a kan £2m, ko da yake za kuma ta iya bayar da aronsa. (Football Insider)

Dan wasan Brazil Hulk, mai shekara 34, ya bar Shanghai SIPG kuma ana rade-radin zai tafi kungiyar da ke buga gasar Firimiyar Ingila. (Sun)

Rahotanni na cewa Tottenham da Arsenal suna son daukar dan wasan AC Milan dan kasar Ivory Coast Franck Kessie, mai shekara 23, wanda za a sayar a kan kusan £45m wanda kuma kwangilarsa za ta kare a watan Yunin 2022. (Calciomercato - in Italian)

Liverpool na fatan soma tattaunawa da dan wasan Brazil Fabinho, mai shekara 27, kan sabunta kwangilarsa nan ba da jimawa ba. (Guardian)

Dan kasar Netherlands Jetro Willems ya yi watsi da tayin sabunta zamansa a Eintracht Frankfurt, inda yanzu Newcastle ta samu damar daukar dan wasan mai shekara 26, wanda ya yi zaman aro a can a kakar wasan da ta wuce. (Chronicle)