An raba jadawalin shiga kofin duniya shiyyar nahiyar Turai

Asalin hoton, Getty Images
Ingila za ta fafata da Poland a rukuni na tara a wasannin neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a 2022 a Qatar.
Sauran wadanda ke cikin rukunin sun hada da Hungary da Albania da Andorra da kuma San Marino.
Tawagar Wales za ta kara da Belgium, wadda ta fitar a gasar nahiyar Turai ta Euro 2016, inda za su kara a rukuni na biyar.
Ireland ta Arewa tana rukuni na biyar da ya kunshi Italy da Switzerland da Bulgaria da kuma Lithuania.
Scotland za ta kece raini da Denmark da Austria da Israel da tsibirin Faroe da kuma Moldova a rukuni na shida.
Ita kuwa Jamhuriyar Ireland za ta yi gumurzu da Portugal da Serbia da Luxembourg da kuma Azerbaijan.
Za a fara wasannin ne tsakanin watan Maris zuwa Nuwambar 2021, sannan a buga wasannin cike gurbi daga Maris din 2022.
Jadawalin wasannin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022.
Rukuni na uku: Italy da Switzerland da Ireland ta Ireland da Bulgaria da kuma Lithuania.
Rukuni na biyar: Belgium da Wales da Jamhuriyar Czech da Belarus da kuma Estonia.
Rukuni na shida: Denmark da Austria da Scotland da Israel da tsibirin Faroe da kuma Moldova.
Rukuni na tara: Ingila da Poland da Hungary da Albania da Andorra da kuma San Marino.
Sakamkon yanayi na zafi a Qatar, gasar kofin duniya da kasar za ta karbi bakunci za a fara daga 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga Disambar 2022.
Hakan zai sa gasar ta zama ta farko da za a gudanar da ita ba a watan Mayu ko Yuni ko kuma Yuli ba.
Za kuma a gudanar da wasannin a kwana 28 da ake sa ran kasashe 32 za su kece raini a filaye takwas a birane biyar da za su karbi bakuncin gasar.
Tawagar kwallon kafa ta Faransa ce ke rike da kofin duniya da ta lashe a Rasha, kuma na biyu da take da shi a tarhi.









