Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar: Dybala, Ronaldo, Trippier, Wan-Bissaka, Ozil, Almada

Asalin hoton, Getty Images
An bai wa manyan kungiyoyin da ke buga gasar Firimiya ta Ingila damar daukar dan wasan Juventus da Argentina Paulo Dybala, mai shekara 27. Kungiyoyin su ne Manchester United, Liverpool, Chelsea, Tottenham, Manchester City da Arsenal. (90 Min)
Manchester United na sanya ido kan dan wasan Atletico Madrid dan kasar Ingila Kieran Trippier, mai shekara 30, a yayin da kocin kungiyar Ole Gunnar Solskjaer yake son dauko dan wasan da zai rika zama a gurbin Aaron Wan-Bissaka, mai shekara 23. (Telegraph)
Kamfanin da ke daukar nauyin kayan wasan Manchester United Chevrolet ya yi amannar cewa ya kamata ya shige gaba wajen dawo da dan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 35, Old Trafford. (Auto Esporte, via Sun)
Dan wasan da ba a damawa da shi a Arsenaldan kasar Jamus Mesut Ozil, mai shekara 32, ya yi amannar cewa zai samu babbar kungiya - amma zai yi wahala ya bar Gunners kafin bazara mai zuwa. (Mirror)
Manchester United ta samu kwarin gwiwar dauko dan wasan Argentina Thiago Almada, mai shekara 19, daga kungiyar Velez Sarsfield. (Todo Fichajes, via Team Talk)
Dan wasanLiverpool da Netherlands Georginio Wijnaldum, mai shekara 30, ya bayyana cewa yana jiran kungiyar ta tuntube shi a kan tsawaita zamansa. (Mirror)
Za a iya tilasta waArsenal ta soma zawarcin Dominik Szoboszlai idan aka bude kasuwar cinikin 'yan kwallo a watan Janairu bayan rahotanni sun nuna cewa Real Madrid na shirin daukar dan wasan na Salzburg mai shekara 20 dan kasar Hungary. (Express)
Daraktan wasanni naParis St-Germain Leonardo ya yi watsi da rahotannin da ke cewa suna son daukar dan kasar Argentina Lionel Messi mai shekara 33 idan ya bar Barcelona a shekara mai zuwa. (Mail)
West Ham na cikin manyan kungiyoyin Ingila da ke son daukar tsohon dan wasan Tottenham Marcus Edwards, wanda a yanzu haka yake kungiyar Vitoria Guimaraes ta kasar Portugal . (Team Talk)









