Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Fernandes, Lingard, Lukaku, Balotelli, Stones, Mbappe, Tosun

An wallafa

Manchester United ta gama shirin saka wa Bruno Fernandes, dan wasanta na tsakiya mai shekara 26, da sabon kwantiragi wanda za a nunka albashinsa zuwa fam 200,000 a mako domin hana Barcelona da Real Madrid kokarin saye shi. (Sunday Mirror)

Dan wasan tsaiya na Ingila Jesse Lingard mai shekara 27 ya shirya tsaf domin sanar da Manchester United cewa zai bar kungiyar a watan Janairu bayan da wasu kungiyoyin Firimiyar Ingila har da na kasar Scotland kamar Rangers da Celtic suka nuna sha'awar sayen dan wasan. (Team Talk)

Amma a nata bangaren, Manchester United ta ce za ta tsawaita kwantiragin Lingard din na shekara guda - duk da cewa ba ya buga wa kungiyar wasanni na tsawon wani lokaci. (Star on Sunday)

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya bukaci Manchester City su sanar da shi idan suna son sayar da John Stones, dan wasan baya mai shekara 26 kuma dan Ingila. (90 Min)

Inter Milan za ta fara tattaunawa da Romelu Lukaku, tsohon dan wasan Everton da Manchester United kan tsawaita zaman sa a kungiyar bayan da Juventus da wasu kungiyoyin ke neman saye shi.. (90 Min)

Tsohon dan wasan Liverpool da Manchester City Mario Balotelli na daf da sanya hannu kan kwantiragi domin buga wa AC Monza, wadda ke wasa a Gasar Serie B har zuwa karshen wannan kakar wasa ta bana. (Sky Sports)

Daraktan wasanni na Paris St-Germain Leonardo ya ce kungiyar na ganin haske kan kokarinsu na tsawaita zaman Kylian Mbappe, dan wasan Faransa mai shekara 21 a kungiyar. (Goal)

Shugaban kungiyar Besiktas Ahmet Nur Cebi ya yarda cewa zai so ya sayo Cenk Tosun, dan wasa Everton mai shekara 29 amma ya na ganin ba za su iya biyan farashin da aka saka ba, sai dai idan za su yi aronsa. (Liverpool Echo)

Jose Mourinho ya ce Tottenham "ba mu bata lokacinmu ba" wajen neman Willian, dan wasan Brazil mai shekara 32 saboda kudin da Arsenal ke bukata kan dan wasan ya fi karfin su. (London Evening Standard)

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya tuntubi Dominik Szoboszlai dan wasan tsakiya na RB Salzburg, yana fatan dan wasan mai shekara 20 zai so komawa kungiyar Sfaniyar. (Bild, via AS)