Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Messi, Barnes, Ings, Winks, Dembele, Diallo

An wallafa

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayo Lionel Messi, dan wasan Argentina mai shekara 33 daga Barcelona a watan Janairu mai shigowa. (ESPN)

Manchester United na fatan Harvey Barnes, dan wasan Leicester mai shekara 22 zai koma kungiyar a matsayin dan aro idan ba ta iya sayo Jadon Sancho ba daga Borussia Dortmund.(Sun)

An ba dan wasan gaba na Ingila Danny Ings mai shekara 28 shawarar tsawaita kwantiragisa da Southamptom. Manajansa Ralph Hasenhuttl ne ya ba shi wannan shawarar. (Sky Sports)

Dan wasan Tottenham Harry Winks mai shekara 24 na iya komawa wata kungiya a watan gobe domin inganta damarsa ta samun shiga kungiyar kwallon kafa ta Ingila gabanin gasar zakarun Turai. (Mirror)

Manchester United ta tattauna da wakilin Ousmane Dembele, dan wasa gaba na Faransa mai shekara 23 domin ganin ko zai koma can yayin da aka bude kasuwar 'yan wasan kwallon kafa a watan goben. (Mundo Deportivo, via Manchester Evening News)

Ole Gunnar Solskjaer ya yi watsi da ikirarin da wasu ke yi cewa kungiyar sa ta Manchester United tana gaba kuma tana yin baya a gasar Firimiyar Ingila. (Sky Sports)

Manchester United na iya gwada sa'arta wajen dauko Thomas Tuchel, kocin Paris St-Germain idan ta kori kocinta Solskjaer a makonni masu zuwa. (Bild)