Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona ba za ta iya biyan albashin 'yan wasa a Janairu ba
Shugaban rikon kwarya na Barcelona, Carlos Tusquets, ya ce kungiyar ba za ta iya biyan albashin 'yan wasanta a watan Janairu ba.
Hakan ya faru ne sakamakon matsin tattalin arziki da kungiyar ta fada a ciki sanadin cutar korona.
A makon jiya Barcelona ta sanar da cimma yarjejeniya da 'yan wasa kan rage albashi domin ya yi daidai da yadda mahukuntan La Liga suka tsara.
"Ba za mu iya biyan albashin watan Janairu ba ..." kamar yadda Tusquets ya shaida wa gidan rediyon RAC1.
"Za mu jinkirta biyan albashin watan Janairu da biyan kudin ladan lashe kofi zuwa nan gaba."
Sai dai kuma Tusquets bai fayyace watan da za su biya albashin na Janairu ba, sai dai ya ce kungiyar za ta ci gaba da tsimi wajen kashe kudi har zuwa karshen kakar bana.
Shugaban ya ce suna sa ran komai zai koma yadda ya kamata da zarar 'yan kwallo sun koma shiga Camp Nou nan gaba kadan.
Barcelona ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League rukuni na bakwai a bana.
Kungiyar ta Camp Nou tana ta bakwai a kan teburin La Liga na bana da maki 14 da kwantan wasa biyu.
Wasannin mako na 12 a gasar La Liga da za a buga:
Juma'a 4 ga watan Disamba
- Athletic Bilbao da Celta de Vigo
Ranar Asabar 5 ga watan Disamba
- Levante da Getafe
- Sevilla da Real Madrid
- Atletico Madrid da Real Valladolid
- Cadiz da Barcelona
Ranar Lahadi 6 ga watan Disamba
- Granada da Huesca
- Osasunada Real Betis
- Villarreal da Elche
- Deportivo Alaves da Real Sociedad
Ranar Litinin 7 ga watan Disamba
- Eibarda Valencia