Ronaldo ya ci kwallo na 750 a sana'arsa ta tamaula

An wallafa

Juventus ta doke Dynamo Kiev da ci 3-0 ranar Laraba a gasar Champions League karawar rukuni na bakwai.

Kungiyar ta Italiya ta fara cin kwallo ta hannun Federico Chiesa a minti na 21, kuma a karon farko da ya zura kwallo a gasar Champions League.

Daga baya ne Cristiano Ronaldo ya ci na biyu a wasan, sannan na 750 da ya zura a raga tun fara sana'ar kwallon kafa.

Alvaro Morata ne ya ci wa Juventus kwallo na uku a minti na 66 da hakan ya sa kungiyar ta hada makinta uku a karawar.

A kuma wasan ne Stephanie Frappart ta zama mace ta farko da ta alkalanci gasar Champions League karawar maza ranar Larabar.

Frappart, mai shekara 36, ta bayar da katin gargadi uku da kin bayar da fenariti da kungiyar Ukraine ta yi korafin ta samu tun kan hutu.

Stephanie Frappart ta fara hura wasa a gasar Zakarun Turai, wadda ita ce ta yi alkalanci wasa tsakanin Liverpool da Chelsea a UEFA Super Cup a bara.

Da wannan sakamakon Juventus wadda tuni ta kai zagaye na biyu a gasar a rukuni na bakwai da Barcelona ce ta daya.

Ita kuwa Dynamo Kiev wadda take ta karshe ta hudu a kasan teburi da maki daya ta yi ban kwana da wasannin bana.

Juventus za ta ziyarci Barcelona a mako mai zuwa don tantance wadda za ta ja ragamar rukuni na bakwai zuwa zagaye na biyu a Champions League na shekarar nan.

Kwallo 750 da Cristiano Ronaldo ya zura a raga a sana'arsa ta kwallon kafa:

  • Real Madrid 450
  • Manchester United 118
  • Portugal 102
  • Juventus 75
  • Sporting Lisbon 5