Real Madrid na fuskantar kalubale a wasannin kakar bana

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Real Madrid na fuskantar kasa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League ta bana.

Real din ta yi rashin nasara a hannun Shakhtar Donesk a Ukraine da ci 2-0, kuma a wasan farko ma Shakhtar cin Madrid ta yi 3-2 a Spaniya.

Cikin rukuni na biyu a gasar Champions League, Real ta koma ta uku da maki bakwai, itama Shakhtar maki bakwai ne da ita a mataki na biyu.

Borussia Monchengladbach ke jan ragamar wannan rukunin da maki takwas, sai Inter Milan ta hudu mai maki biyar.

Hakan na nufi sai a wasan karshe ne za a fayyace kungiyoyi biyun da za su kai karawar zagaye na biyu a gasar bana.

Kuma Real za ta kece raini da Borussia Monchengladbach a wasa na karshe na cikin rukuni ranar 9 ga watan Disamba.

A kuma ranar ce Inter Milan za ta karbi bakuncin Shakhtar Donetsk a Italiya.

Wasu na cewa Zinedine Zidane na cikin matsi na ganin ya samu sakamakon da zai faranta ran mahukuntan kungiyar a bana.

Ko a gasar cikin gida ma Real Madrid tana ta hudu a teburin La Liga da maki 17, bayan da ta buga karawa 10 a gasar Spaniya ta shekarar nan..

Ranar Asabar Alaves ta yi nasara a gidan Real Madrid a gasar La Liga da ci 2-1, sannan ta sha kashi a hannun Shakhtar da ci 2-0 ranar Talata a Champions League.

Wasannin da ke gaban Real Madrid a yanzu haka sune za su fayyace makomar kocin da kungiyar ko za ta yi abin barka.

Ranar 5 ga watan Disamba Real za ta ziyarci Sevilla a gasar La Liga, sannan ta karbi bakuncin Borussia Monmchengladbach a Champions League ranar Laraba 9 ga watan Disamba.

Daga nan Real za ta karbi bakuncin Atletico Madrid a wasa na hamayya a La Liga ranar Asabar 12 ga watan Disamba ta kuma kara da Athletco Bilbao ranar 15 ga watan Disamba.

Hakika Zidane zai fuskanci kalubale idan har Real Madrid ba ta kai zagayen gaba ba a Champions League na shekarar nan.

Haka kuma za a tada jijiyar wuya da zarar ta kasa doke Atletico a wasan hamayya a gasar La Liga.

Tun bayan da aka fara kakar tamaula ta bana cikin watan Satumba, Real ta ci wasa bakwai da canjaras uku aka doke ta wasa biyar.